Editor

9513 Posts
Azabtar da ‘ya’yan miji da sunan kishi

Azabtar da ‘ya’yan miji da sunan kishi

Daga SADIYA GARBA YAKASAI 'Ya'yan kishiyoyi: Yau zan yi magana akan zaman kishi, ma'ana yadda wasu matan ke mai da yaran kishiyoyinsu bayi ko su fifita nasu a kan na kishiyarsu da ba sa tare. Wasu ma suna tare da iyayen yaran, amma ba su da kataɓus a gidan. Wala'alla ta fi ƙarfin mijin, bai da yadda zai yi da ita, sai abin da ta ce. Ko kuma ta shiga ta fita ta raba uban da yaransa, bai ganin komai sai ita sai yaranta. Wannan ɗabi'a ta zama jiki ko na ce ta jima tana yawo gidajen masu mata fiye…
Read More
Kasuwanci: Matakan dawo da martabar Kano da Buhari da Ganduje ke bi

Kasuwanci: Matakan dawo da martabar Kano da Buhari da Ganduje ke bi

Ƙaddamar da aikin aikin shimfiɗa layn dogo daga Kano zuwa Kaduna, wanda Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a kwanan nan da kuma ƙaddamar da gada mai hawa uku, wacce Gwamnatin Jihar Kano a ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, alama ce ta yadda Buhari da Ganduje ke fafutukar ganin sun dawo da martabar Kano a idanun duniya bakiɗaya ta fuskar kasancewar ta jagabar kasuwanci a yankin Afrika ta Yamma. Layin dogon na daga cikin wani ɓangare na aikin tabbatar da shimfiɗa shi daga Kano zuwa Legas, inda a ka fara aikin shimfiɗa gadar jirgin ƙasa ta zamani daga Abuja…
Read More
Zuwan Buhari jinya a ƙetare ba gazawa ba ne ga fannin kiwon lafiyar Nijeriya, cewar Lai

Zuwan Buhari jinya a ƙetare ba gazawa ba ne ga fannin kiwon lafiyar Nijeriya, cewar Lai

Ministan Yaɗa Labarai da Raya Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana cewa tafiya ƙetare da Shugaba Muhammadu Buhari kan yi don kula da lafiyarsa, hakan ba yana nufin fannin kiwon lafiyar Nijeriya ya durƙushe ne ba. Ministan ya bayyana hakan ne yayin tattauna da wasu manyan kafafen yaɗa labarai na duniya da suka haɗa da BBC da Bloomberg da kuma Politico, a Amurka. Kamafanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa, Minista Lai ya ziyarci Amurka ne don ganawa da manyan kafafen yaɗa labarai kan abin da ya shafi irin nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu da kuma ƙoƙarin da…
Read More
Buhari ya bayyana waɗanda za su wakilce shi a wajen ɗaurin auren ɗansa da bikin sarautar Sarkin Bichi

Buhari ya bayyana waɗanda za su wakilce shi a wajen ɗaurin auren ɗansa da bikin sarautar Sarkin Bichi

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana sunayen tawagar da za su wakilce shi wajen ɗaurin auren ɗansa Yusuf Buhari da 'yar Sarkin Kano, Zahra Bayero wanda za a yi a yau Juma'a a Kano. Kazalika, tawagar ce za ta sake wakiltar Shugaban Ƙasa wajen bikin sarauta na Sarkin Bichi da zai gudana gobe Asabar idan Mai Duka Ya kai mu. Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Alhamis. Shehu ya ce, tawagar za ta wakilci Shugaban Ƙasa ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Farfesa Ibrahim…
Read More
HOTUNA: Taron horar da ma’aikatan hukumar NAHCON

HOTUNA: Taron horar da ma’aikatan hukumar NAHCON

Ranar farko kenan ta bada horo kan shirin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da 'yan kasuwa (PPP) wajen gina al'umma, wanda hukumar ICRC ta shirya a babban zauren taro na Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) a ranar Laraba. Mahalarta taron sun haɗa da Shugaban hukumar NAHCON na ƙasa, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, Kwashinan NAHCON, Alhaji Abdullahi Magaji Hardawa da sauran ma'aikatan NAHCON Staff. Zauren taro Zauren taro Zauren taro
Read More
Gwamnati ta nemi kotu ta janye haramcin kamo Igboho

Gwamnati ta nemi kotu ta janye haramcin kamo Igboho

Babban Lauyan Nijeriya, Abubakar Malami, ya miƙa wa Babbar Kotun jihar Oyo takarda ta neman tsallake dokar hani da kotu ta gindaya da ta hana kama Sunday Adeyemi (Sunday Igboho) da kuma daƙile asusunsa na banki. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya ruwaito a ranar 4 Agusta, kotun ta aminta da buƙtar da Igboho ya nema ta hana hukumar DSS da Babban Lauyan Ƙasa su damƙe shi da kuma daƙile masa asusunsa na banki. Tun farko lauyan Igboho, Mr Yomi Aliyu, ya shaida wa kotu cewa rayuwar wanda yake karewa na fuskantar barazana tun bayan da DSS ta kai wa…
Read More
Cutar korona: Nijeriya ta karɓi tallafin rigakafin AstraZeneca 699,760 daga Birtaniya

Cutar korona: Nijeriya ta karɓi tallafin rigakafin AstraZeneca 699,760 daga Birtaniya

A Talatar da ta gabata Nijeriya ta karɓi allurar rigakafin korona samfurin AstraZeneca-Oxford guda 699,760 ta hannun COVAX a matsayin tallafi daga Ƙasar Birtaniya. Muƙaddashin jakadan Birtaniya a Nijeriya, Gill Atkinson tare da sauran manyan jami'ai ne suka ya yi tarayya da shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Nijeriya, Dr Faisal Shuaib, wajen ƙaddamar da rigakafin. An ƙaddamar da maganin ne a ɗakin sanyi na ajiyar magunguna da ke daura da Babban Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja. Rigakafin da Nijeriya ta karɓa ɗin wani ɓangare ne na rigakafin AstraZeneca ƙwaya milyan uku da…
Read More
Minista Lai ya saci jiki zuwa Amurka don ganawa da shugabannin Tiwita

Minista Lai ya saci jiki zuwa Amurka don ganawa da shugabannin Tiwita

Sahihan rahotanni sun tabbatar da Ministan Yaɗa Labarai da Raya Al'adu na Nijeriya, Lai Mohammed ya tafi Ƙasar Amurka musamman don ganawa da shugabannin kamfanin Tiwita. Cikin wani hoton bidiyo da aka yaɗa jiya Talata, an ga Minista Lai tare da Olusegun Adeyemi wanda hadimi ne na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga ga Shugaban Ƙasa, a cikin jirgin sama na Delta Airline za su keta hazo zuwa Amurka. Idan dai za a iya tunawa a ranar 5 ga Yulin da ya gabata ne Gwamnatin Nijeriya ta haramta wa kamfanin Tiwita gudanar da harkokinsa a Nijeriya baya da Tiwita ta…
Read More
Kisan Musulmi a Rukuba: Sarkin Musulmi ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Filato

Kisan Musulmi a Rukuba: Sarkin Musulmi ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Filato

Daga AMINA YUSUF ALI Majalisar Addinin Musulunci ta Ƙasa a ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III (JNI) ta yi kira ga Gwanmatin Jihar Filato da ta nemo masu aika-aikar kisan Muslmin Rukuba, don a gurfanar da su. A cewar majalisar, wannan al'amari ya nuna ƙololuwar rashin wayewa inda Ƙungiyar Jama'atu Nasrul Islam ta yi kira ga gwamnatin jihar filato da ta yi gaggawar bincikowa tare da hukunta waɗanda suke da hannu acikin wannan mummunan aikin na kisan musulmi a hanyar Rakuba. A wata takardar jawabin manema labarai da ƙungiyar ta wallafa, wacce take ɗauke da sa…
Read More