Bankin raya ƙasar Sin ya yi matuƙar taimaka wa ci gaban makamashi mai tsafta a rubu’in farkon bana

Daga CMG HAUSA

Bankin raya ƙasar Sin (CDB), ya ninka kuɗaɗen tallafawa ayyukan samar da makamashi mai tsafta a rubu’in farko na wannan shekarar da muke ciki.

A cewar bankin na CDB, ya fidda rancen kuɗi da yawansa ya kai kuɗin Sin RMB yuan biliyan 109, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 17.12, domin tallafawa ci gaban makamashi mai tsafta, da sauya fasalin samar da makamashin da aka saba amfani da su zuwa hanyar kaucewa gurɓata muhalli.

A cikin rubu’in farko na wannan shekara, an samar da rancen kuɗi da ya kai jimillar yuan biliyan 76.5 domin gudanar da ayyukan bunƙasa samar da makamashi mai tsafta da suka haɗa da makamashin nukiliya, da na iska, da makamashin solar mai amfani da hasken rana.

Mai Fassara: Ahmad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *