Bankunan China za su soma karɓar kuɗin Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

A wani mataki na yauƙaƙa dangantaka da kuma haɓaka kasuwanci tsakanin China da Nijeriya, China ta ce bankunan ƙasar za su soma karɓar kuɗin Nijeriya, wato Naira.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Jakadan Ƙasar China a Nijeriya, Cui Jianchun kamar dai yadda mai bai wa Shugaban Ƙasa Mummadu Buhari shwara kan sabbin kafafen yaɗa labarai, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na facebook a ranar Alhamis.

Cui Jianchun ya ce wannan mataki zai taimaka wajen bunƙasawa tare da sauƙaƙa gudanar da harkokin kasuwanci da zuba jari a tsakanin Nijeriya da China.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *