Benzema ya daƙile yunƙurin Barcelona na lashe Copa del Rey

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Real Madrid ta kai wasan ƙarshe a Copa del Rey, bayan da ta doke Barcelona 4-0 a wasa na biyu ranar Laraba a Nou Camp.

Daf da za su je hutu Vinicius Junior ya ci wa Real ƙwallon farko, Karim Benzema ya ƙara na biyu minti biyar da komawa zagaye na biyu.

Tsohon ɗan wasan tawagar Faransa shi ne ya ci na uku, kuma na biyu a wasan hamayya na El Clasico a bugun fenariti.

Daf da za a tashi kenan Benzema ya ƙara na uku na huɗu a wasan, karo na biyu a jere yana cin uku rigis a Real Madrid.

A ƙarshen mako Real ta caskara Valladolid 6-0, inda Benzema ya ci uku rigis a karon farko a bana a Real Madrid.

Real Madrid ta kai zagayen gaba da cin
ƙwallo 4-1 gida da waje, bayan da Barcelona ta yi nasarar cin 1-0 a wasan farko ranar 2 ga watan Maris.

Wasa na biyar kenan da aka kara tsakanin manyan ƙungiyoyin Sifaniya, Barcalena ta yi nasara a uku, Real Madrid ta ci biyu.

Real Madrid za ta buga wasan ƙarshe a Copa del Rey da Osasuna ranar Asabar 6 ga watan Mayu.

Osauna ta kai wasan ƙarshe da cin Athletic Bilbao 2-1 gida da waje, bayan da suka tashi 1-1 a wasa na biyu ranar Talata, a fafatawar farko Osasuna ta ci 1-0.

Karon farko da Osasuna za ta buga wasan ƙarshe a Copa del Rey tun bayan 2005.

Real Betis ce mai riqe da Copa del Rey na bara, Real Madrid tana da shi 19, Barcelona ce kan gaba a yawan ɗaukar kofin mai 31 jimilla.

Barcelona ce ta ɗaya a kan teburin La Liga da tazarar maki 12 tsakaninta da Real Madrid ta biyu.

Ranar Asabar 8 ga watan Afirilu, Real Madrid za ta karɓi baƙuncin Villareal a wasan La Liga, kwana hudu tsakani ta kece raini da Chelsea a daf-da-kusa-da-ƙarshe na gasar Zakarun Turai a Sifaniya.

Ranar Litinin 10 ga watan Afirilu Barcelona za ta kece raini da Girona a La Liga a Nou Camp.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *