Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Jarumi Adam A. Zango

Daga LARABI LARABEEN

Zuwa ga jarumi Adam A. Zango, Ina fata wasiƙata ta same ka cikin ƙoshin lafiya. Game da maganar da ka yi cewa, ba za ka ƙara aure ba har abada, haba don Allah! Bai kamata ka ce haka ba. Da ma tin filazal fitattun mutane kan sha fama da matsaloli kala-kala. Amma kai naka kuskuren ya samo asali a kan yadda kake zaɓen macen aure mai kyawu fuska fiye da kyawun ɗabi’a da tarbiyya.

Wata matsalar taka kuma ita ce, ka daina auren macen da take son Adam A. Zango na Film. Ka nemi macen da take son Adamu na Zahiri da take gani. In da hali ma wacce ba ta damu da kallon fina-finan Hausa ba.

Na tava ayyanawa a raina sanda nake tashen rubuta Littatafan soyayya na Hausa. Lokacin ina Tashe. Mata Kyawawa da ɗiyan masu kuɗi da sarauta da mulki na rububina. Suna kawo min ziyara har gida ko su gayyace ni na je har gidajensu ko mu haɗu a wani Joint a sha abin sha da shawarma lokacin shawarma tana shawarma. Wajejen 2000 zuwa 2006.

Na yi slkawarin duk tarin mata masoyana ba zan auri ko ɗaya cikin masu so na da aure ba. Kuma ba zan Taɓa Yarda iskanci ya haɗa ni da wata ba. Sai dai a yi mutunci kawai da zumunci. A haka na samar wa kaina lafiya daga kaidin mata masu karanta littafina.

Akwai Wadda ta tava zuwa Tun daga harinsu bangon Nikeriya. Ta kwashe ni da direbansu a motar gidansu. Ba ta dire ni ko’ina ba sai gidansu, falon Babansu wai tana so na. Za ta aure ni.

A lokacin ta fi ƙarfin ajina. Saboda Kyakkyawa ce sjin farko. Shekarunmu banbancinsu ba yawa sosai. Ta fi ni wayo da wayewa gami da gogewa. Ina kin idan Anti Bebi Umma Sulaiman Y’an Awaki tawa za ta iya tunawa, na kai mata yarinyar har gida wajejen 2005 zuwa 2006.

Yarinyar ta dage tana son aurena. Babansu ya yi intabiyu. Na zille don sama wa kaina lafiya.

Bayan ita na yi ‘yammata da yawan gaske. Ko Ibrahim Muhammad Indabawa ya ci awara da kayan maƙulashe shi da Usman Ya’u Ango na wata budurwa da ta dinga yi min hidima tana aiko min daga garinsu.

Jamila Umar Tanko ta ci Kaji da kayan maqulashe na wata da ta dinga yi min hidima.

Wasu matan suna so na ne da zaton ni ma LARABI irin hali da siffa da komai irin na tauraron da na siffanta a cikin littafina ne.

Wani abu da mutane ba su cika ganewa ba shi ne, ba aure kaɗai ba ko abota ce aka qulla ta da wata manufa ba don Allah ba wallahi ana samun matsaloli sosai ƙarshe dole a ɓaɓe.

Bare kuma aure. Duk wanda ya yi aure don wata manufa ba ta ibada ba, ba domin Allah ba, tabbas wallshi sai ya sha wahala.

Aure Bautar Ubangiji ce wanda in ka sa a ranka za ka yi don biyayya gare shi to tabbas za ka ji daɗin auren ko da ana samun matsaloli can da can. Idonka zai rufe ba za ka dinga kallonta a matsayin matsala ba.

Sannan abu na ƙarshe da muke yaudarar kanmu da shi shi ne, jin wasu na cewa su ba su da matsala a gidajen aurensu. Ƙarya suke yi. Kowane aure akwai irin tasa matsalar sai dai wasu suna da kau da kai. Wasu suna da juriya da Haƙuri. Kai wani ma laifin za ai masa ya nuna ai ba laifi ba ne.

Sai batun Lafiya da wasu ke ta yamadidi wai ko ba shi da lafiya.

To a ɗan binciken da na yi lokacin da na fara siyar da magungunan ƙarfin mazakuta da na basir da sanyi, Kaso 65% na Maza suna da wannan lalurar ta saurin kawowa. Sai dai kowa da irin nasa. Sannan da yawa ba lalurar ke kawo hakan ba. Rashin ilmin jima’i ne da rashin ilmin aure ke jawo hakan. Akwai wanda Kwarjinin macen ke sashi saurin kawowa.

Akwai wanda zaƙuwa ne. Da yawanmu baqaqen fata ba ma zuwa ga jima’i sai lokacin da muke da buwata. Wannan ma na haifar da saurin Kawowar.

Sannan da yawanmu baƙaƙen fata muna ɗaukar jima’i shi ne kaso 85% na rayuwar aure shi ya sa yake ba mu wahala. Wanda kuma ba haka ba ne.

Sannan akwai gajiya, rashin samun wadataccen jutu na jiki ko na ƙwaƙwalwa ko na zuciya.

Akwai kuma yawan jutun ma kansa. Da sauran matsaloli dai barkatai.

Idan kuma Allah ya sa wannan runutun zai riski Adam A. Zango kuma ya karanta, akwai shawarwari masu yawa da zan iya ba shi ta kowacce fuska wajen zaɓen mace ta gaba da zai aura. Hatta ga lafiyar auratayya ɗin akwai magunguna ko shawarwari da zan iya ba shi kuma Insha Allahu zai dace.

Kar ya ce ya daina Aure har abada. Aure sutura ce ta kowane baligi idan har yana da ikon yi. Sannan kowane ɗan Adam yana da irin kalar tasa ƙaddarar.

Bissalam.

Larabi Larabeen (UNCLE LARABI) Alhaji Larabi marubuci ne kuma mai sharhi. Ya rubuto daga jihar Kano.
Lambar waya: 08065418892

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *