Bunƙasa lantarki: Nijeriya za ta karɓi rancen Dala miliyan 200 daga Japan

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnati Tarayyar Nijeriya ta bayyana ƙudurinta na amso rancen Dalar Amurka Miliyan 200 daga hukumar haɗakar kamfanoni  na ƙasar Japan (JICA). Gwamnatin ta bayyana cewa, ba wani abu za ta yi da kuɗaɗen ba illa ta ƙara ƙarfin wutar lantarki a wasu zaɓaɓɓun ɓangarori a cikin jihohin Ogun da Legas.
 
Alhaji Abubakar Aliyu, Ministan Makamashin Nijeriya, shi ya bayyana haka, a yayin da yake amsar baƙuncin wasu wakilai daga hukumar ta JICA a ofishinsa dake birnin tarayyar Abuja, inda ministan ya ƙara da cewa, wannan yunƙuri an yi shi ne domin a ƙara inganta sashen samar da wutar lantarki a ƙasar Nijeriya.

A cewar Ministan, wannan shirin bunƙasa wutar lantarki wanda hukumar wutar lantarki ta Nijeriya za ta gudanar, za a samar da wutar lantarki mai ƙarfin Kilo 203, wanda ƙananan hukumomi guda 5 daga jihar Ogun da kuma ƙaramar hukuma 1 a jihar Legas ne za su amfana. Wato ƙiyasin unguwanni ɗari biyu ne za su amfana. 

A cewarsa, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da kuma Hukumar JICA za su haɗa gwiwa wajen ganin hakan ta tabbata, domin ko ba komai, samar da isasshiyar wutar lantarki zai taimaka wajen bunqasar masana’antu a jihohin Legas da Ogun.