09
Jan
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano A Asabar ɗin da ta gabata, 25 ga Disamba, 2021, ne aka ɗaura aure tare da ƙaddamar da littafi mai suna Ruwan Jakara, wanda marubuci kuma Editan jaridar Blueprint Manhaja, wato Nasir Sa'ad Gwamgwazo, ya rubuta. An dai ɗaura auren ne a Masallacin Wudilawa da ke kusa da gidan Sarkin Kano, daura da Gidan Makama, yayin da aka yi walima da ƙaddamar da littafin a babban ɗakin taro na Kannywood TV da ke unguwar Tudun Yola kusa da Ƙofar Kabuga akan hanyar zuwa Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke cikin birnin Kano. Tun da farko a…
