16
May
Daga JOHN D.WADA LAFIYA Jihar Nasarawa dai na ɗaya daga cikin jihohin Nijeriya da a baya aka yi ta samun rigingimu tsakanin makiyaya da manoma. A yanzu da aka shiga daminar bana, Wakilin Blueprint Manhaja, John Wada Lafiya, ya samu tattauna da Shugaban Ƙungiyar nan ta Miyetti Allah Cattle Breeders ta ƙasa reshien Jihar Nassarawa, Alhaji Bala Mohammed Dabo, a ofishinsa da ke sakatariyar ƙungiyar a jihar. Tattaunawar ta kasance dangane da matakai da qungiyar ta ɗauka, don hana afkuwar rigirgimun tsakanin ɓangarorin biyu a bana. Ga dai yadda tattaunawar ya kasance: MANHAJA: Rankayadade, damina ta sake zagayowa. Kuma a…
