15
Nov
Daga MOHAMMED ALI a Gombe Alhaji Lamido Muhammad, wanda aka fi sani da Sarkin Yaƙi, shine Shugaban Rundunar Maharba na yankin Akko a Ƙaramar Hukumar Akko da ke cikin Jihar Gombe. Shi dai Alhaji Lamido ya yi suna da tasiri, saboda irin bajitarsa da gwagwarmaya a cikin dazuzzukan Gombe, musamman dazuzzukan Akko, wurin da ya yi fice saboda ƙungurumin dazuzzuka masu cike da dabbobi da iskokai wasu halitttun ɓoye waɗanda a cewar maharba sai ka shirya za ka iya shiga cikin su. To amma, Alhaji Lamido shi waɗannan dazuzzuka tamkar gari ne ko gida a wurin shi. 'Na shige su…
