16
Jun
Daga CMG HAUSA A yammacin yau ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na ƙasar Rasha Vladimir Putin. Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, ƙasar Sin na son hada kai tare da ƙasar Rasha, wajen inganta hadin gwiwarsu ta hanyar da ta dace. Ƙasar Sin tana son ci gaba da nuna goyon baya ga ƙasar Rasha kan batutuwan da suka shafi muhimman muradunsu, da manyan batutuwan da suka shafi harkokin ikon mulkin ƙasa, da tsaro, da yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin ƙasashen biyu, da ƙarfafa tattaunawa da yin haɗin gwiwa…
