Kasashen Waje

CMG ya ƙaddamar da aikin kafofin watsa labarai na kare muhalli na Sin da Afirka

CMG ya ƙaddamar da aikin kafofin watsa labarai na kare muhalli na Sin da Afirka

Daga CMG HAUSA A yayin bikin "Ranar Muhalli ta Duniya" da aka yi a yau Lahadi, an kaddamar da "Aikin kafofin watsa labarai na kare muhalli na Sin da Afirka" a hukumance, wanda sashen babban gidan rediyo da talabijin na ƙasar Sin wato CMG dake nahiyar Afirka ya ƙaddamar a Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya. A yayin bikin ƙaddamar da aikin, CMG da muhimman kafofin watsa labaru na wasu ƙasashen Afirka da dama, sun gabatar da shawarar "Yin murya domin muhallin halittu" tare, inda aka yi kira ga kafofin watsa labaru na ƙasar Sin da na Afirka da su haɗa…
Read More
Xi Jinping ya aike da wasiƙar taya murna ga bikin ƙasa na ranar muhalli ta shekarar 2022

Xi Jinping ya aike da wasiƙar taya murna ga bikin ƙasa na ranar muhalli ta shekarar 2022

Daga CMG HAUSA Yau Lahadi, an shirya bikin ranar Muhalli ta ƙasa na shekarar 2022 a birnin Shenyang na lardin Liaoning dake Arewa maso gabashin ƙasar Sin. Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya aike da wasiƙar taya murna domin nuna farin cikinsa kan gudanar da bikin. A cikin wasiƙar, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, muhallin halittu shi ne ginshikin rayuwa da ci gaban dan Adam, kuma kiyaye muhalli yadda ya kamata shi ne burin bai ɗaya na jama'ar ƙasashe daban daban. A cewarsa, tun bayan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, kasar Sin…
Read More
Masanin ilmin muhalli na Zimbabwe: Hanyar raya ƙasar Sin ba tare da gurɓata muhalli ba ta zama abin koyi Glga duniya

Masanin ilmin muhalli na Zimbabwe: Hanyar raya ƙasar Sin ba tare da gurɓata muhalli ba ta zama abin koyi Glga duniya

Daga CMG HAUSA Masanin ilmin muhalli na ƙasar Zimbabwe, Courage Tavenhave ya yabawa matakan da ƙasar Sin take ɗauka na raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar ƙasa da kuma muhalli. Courage Tavenhave, ya bayyana haka ne yayin da ya zanta da wakilin babban gidan rediyo da talibijin na ƙasar Sin CMG a baya-bayan nan, yana mai cewa, matakan ƙasar Sin na neman raya ƙasa ba tare da gurɓata muhalli ba, da kuma kyawawan fasahohinta, sun cancanci ƙasashen duniya su yi koyi da su. Masanin ya bayyana cewa, a shekarun baya bayan nan, ƙasar Sin ta rubanya ƙoƙarinta na kara azama…
Read More
Ƙasar Sin ta bayyana ayyukan da ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14 za su yi a sararin samaniya

Ƙasar Sin ta bayyana ayyukan da ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14 za su yi a sararin samaniya

Daga CMG HAUSA Hukumar kula da kumbuna ta ƙasar Sin, ta ce ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14 da za a tura, za su kammala aikin ginin cibiyar binciken sararin samaniya ta Tiangong, wanda ya kunshi muhimman ɓangarori 3, wadanda suka haɗa da babban ɓangaren cibiyar na Tianhe da kumbunan ɗakunan gwaji na Wentian da Mengtian. A cewar mataimakin daraktan hukumar, Lin Xiqiang, ‘yan sama jannatin za su yi aikin gina cibiyar ta sararin samaniya zuwa ɗakin gwaje- waje na ƙasar a sararin samaniya. ƙasar Sin ta shirya harba kumbon Shenzhou-14 ne a gobe Lahadi, daga cibiyar harba tauraron dan Adam…
Read More
Shinkafa mai inganci ta ƙasar Sin ta bada gudunmuwa wajen ƙara yawan shinkafa a Nijeriya

Shinkafa mai inganci ta ƙasar Sin ta bada gudunmuwa wajen ƙara yawan shinkafa a Nijeriya

Daga CMG HAUSA A yayin wani taron da aka gudanar a ranar 2 ga wata dangane da taimakawa ƙasashen yammacin Afirka kafa wani tsarin noman shinkafa, Wang Xuemin, mai taimakawa babban darektan kamfanin Green Agriculture West Africa wato GAWAL ƙarƙashin shugabancin kamfanin CGCOC kuma masanin ilmin noman shinkafa, ya yi ƙarin bayani kan yawan shinkafar da ake girbewa bisa mabambantan fasahohin noma da kuma amfani da mabambantan irin shinkafa a wasu gonaki. A shekarun baya, gwamnatin Najeriya ta bada muhimmanci kan noman shinkafa a ƙasar, ta kara zuba jari da taimakawa masana’antun shinkafa ta fuskar manufofi, sa’an nan ta mai…
Read More
Kamata ya yi ‘yan siyasar Amurka masu cewa suna martaba al’ummar Sinawa su dakatar da kitsa ƙarairayi

Kamata ya yi ‘yan siyasar Amurka masu cewa suna martaba al’ummar Sinawa su dakatar da kitsa ƙarairayi

Daga CMG HAUSA Cikin jawabin sa na baya bayan nan game da manufofin ƙasar Sin, sakataren wajen Amurka Antony Blinken, ya ce Amurka na da manyan bambance bambance tsakanin ta da JKS, da ma gwamnatin ƙasar Sin, amma waɗannan bambance bambance na da nasaba ne da gwamnatocin ƙasashen, da tsarin gudanarwa, ba wai da al’ummun sassan biyu ba. Sai dai waɗannan kalamai na Mr. Blinken, ba za su samu karɓuwa a kunnuwan Sinawa, da al’ummun ƙasa da ƙasa, da ma shi kan sa Blinken ba. Kasancewar su ƙarya ce tsagwaron ta! Idan da gaske ne, kamata ya yi ‘yan siyasar…
Read More
Kalaman Xi Jinping game da kishin ƙasa

Kalaman Xi Jinping game da kishin ƙasa

Daga CMG HAUSA A bana yau Juma’a ce ranar da Sinawa ke murnar bikin Duanwu. An fara gudanar da wannan biki na musamman ne, domin tunawa da wani shahararren marubucin rubutattun waƙoƙi mai kishin ƙasa mai suna Qu Yuan, wanda ya rayu a zamanin daular Zhanguo wato the Warring States Period a Turance wato tsakanin shekarar 475 zuwa 221 kafin haihuwar Annabi Isa A.S. Qu, ya rubuta waƙoƙi da dama game da rayuwar al’umma da kishin ƙasa, kuma shugaban ƙasar Sin, babban sakataren kolin JKS, kana shugaban hukumar gudanarwar rundunar sojojin ƙasar Xi Jinping, ya kan tsamo wasu kalmomin dake…
Read More
Yadda ƙasar Sin ta yi nasarar sauƙaƙa fatara da raya karkara a gomman shekaru

Yadda ƙasar Sin ta yi nasarar sauƙaƙa fatara da raya karkara a gomman shekaru

Daga: LAWAL SALE Sanin kowa ne cewa Sin ƙasa ce wacce ta ɗauki yaƙi da fatara da muhimmanci, musanmman ma a yankunan karkara inda masu fama da ƙangin talauci suka fi yawa. Sin dai ƙasa ce mai tasowa da ta fi kowace girma a duniya kuma tana gaba-gaba a kan yaƙi da fatara ko kuma talauci a yayin da ta ɗauki matakai waɗanda suka sa ta kawar da ƙangin talauci daga dukkan fannoni zuwa shekarar 2020. Wannan cimma nasara dai yana da inganci mai yawa a rayuwar jama’a, da tattalin arziki, da yanayin tsarin gudanar da mulki. Matakan dai da…
Read More
Yaƙi da COVID-19 a Shanghai: Kwalliya ta biya kuɗin sabulu

Yaƙi da COVID-19 a Shanghai: Kwalliya ta biya kuɗin sabulu

Daga SAMINU ALHASSAN Tun bayan fara aiwatar da matakan kullen annobar COVID-19 da ta ɓarke a birnin Shanghai na ƙasar Sin, kimanin watanni 2 da suka gabata, a yanzu haka mahukuntan birnin mai yawan al’umma sama da miliyan 25, sun ce matakan da aka ɗauka sun haifar da “da mai ido”, kuma “kwalliya ta biya kuɗin sabulu”. Tuni dai aka sanar da tsara sake buɗe birnin, inda ake sa ran daga Alhamis din nan 2 ga watan Yuni, za a buɗe hanyoyin shiga unguwanni, kana za a dawo da ayyukan sufuri da zirga-zirgar ababen hawa, waɗanda dukkanin su matakai ne…
Read More
Kamfanonin ƙasar Sin sun bada kyauta ga ɗaliban Ghana da ke fama da talauci

Kamfanonin ƙasar Sin sun bada kyauta ga ɗaliban Ghana da ke fama da talauci

Daga CMG HAUSA Wasu kamfanoni biyu na ƙasar Sin, sun baiwa wasu ɗaliban makarantun firamare dake ƙasar Ghana kyauta, albarkacin bikin ranar yara ta duniya da aka shirya a birnin Jamestown, daya daga cikin al'ummomin da ke fama da talauci a Accra, babban birnin ƙasar Ghana. Kamfanin CRCC Harbor da kamfanin CCCC First Harbor Consultants CO., LTD, sun ba da gudummawar gwomman kwallayen kafa, da jakunkuna na makaranta, da fensira masu launi, da abin goge rubuta, da sauran kayan makaranta masu yawa ga makarantar reno ta Chirst the king of kings, wadda ke kusa da tashar kamun kifi ta Jamestown…
Read More