08
Jun
Daga CMG HAUSA Larabar nan ce, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci birnin Meishan na lardin Sichuan dake yankin kudu maso yammacin ƙasar. Da safiyar yau, Xi ya ziyarci ƙauyen Yongfeng da San Su Ci, wurin tunawa kuma tsohon mazaunin Su Xun da 'ya'yansa maza guda biyu Su Shi da Su Zhe, mashahuran mutane uku wajen adabi na zamanin daular Song ta Arewa (960-1127). Xi ya kuma fahimci ƙoƙarin da ake yi wajen bunƙasa manyan filayen noma, da bunƙasa noman hatsi, da inganta farfaɗo da yankunan karkara, da kiyaye muhimman matakan kandagarki da daƙile yaduwar COVID-19, da kiyaye kayayyakin…
