Labarai

Za mu ci gaba da jajircewa wajen hidimta wa jama’a vangaren kiwon lafiya – Kwamared Yusuf

Za mu ci gaba da jajircewa wajen hidimta wa jama’a vangaren kiwon lafiya – Kwamared Yusuf

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Shugaban Asibitin PHC Kabuga, Yusuf Adamu Muhammad Kabuga a Ƙaramar Hukumar Gwale ya bayyan cewa karrama shi da lambar yabo abin farin ciki ne gare shi da ma'aikatan asibitin Kabuga PHC, da sashin lafiya na ƙaramar hukumar Gwale da ma'aikatar lafiya da sauran masu ruwa da tsaki na Kano kamar yadda Kwamared Yusuf Adamu Muhammad ya bayyana a lokacin da ya karɓi kyautar karramawa ga ƙungiyar Health Awareness a makon da ya gabata. Haka kuma Malam Yusuf ya ce aikin lafiya aiki ne na jama'a da ke buƙatar kulawa da nutsuwa, da haƙuri da jajircewa,…
Read More
Ofishin jakadancin Falasɗinu a Nijeriya ya yi Allah-wadai da kisan da Isara’ila ke yi wa Falasɗinawa

Ofishin jakadancin Falasɗinu a Nijeriya ya yi Allah-wadai da kisan da Isara’ila ke yi wa Falasɗinawa

*Ya nuna alhini kan sace ɗaliba a arewacin Nijeriya Daga BASHIR ISAH Ofishin Jakadancin Falasɗinu a Nijeriya ƙarƙashin Abdullah M. Abu Shawesh, ya tir da irin kisan kiyashin da Isra'ila ke yi wa Falasɗinawa. Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a, ofishin ya fara bayani ne da nuna alhininsa kan ɗaliban da aka sace da sauransu a yankin Arewa. Abdullah M. Abu Shawesh ya ce, "Jin irin wannan labari yana motsa ni sosai kuma yana ƙara baƙin cikina "A cewar dokar Yahudawa, dole ne a kashe dukkan mazauna Gaza." "Hukumomin Isra'ila sun amince da wannan nau'in tunzura jama'a, kuma…
Read More
RTEAN ta ƙaddamar da sabbin shugabannin Legas

RTEAN ta ƙaddamar da sabbin shugabannin Legas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar ma’aikatan motocin sufuri ta qasa (RTEAN) reshen jihar Legas ta ƙaddamar da sabbin shugabannin ƙungiyar ta ƙasa. Ku tuna cewa an dakatar da ayyukan RTEAN a jihar Legas sama da watanni 15. Bayan shiga tsakani da gwamnatin tarayya ta yi, an shawo kan lamarin wanda ya kai ga sake fasalin shugabannin ƙungiyar a jihar. A lokacin da yake jawabi ga sabbin zaɓaɓɓun shugabannin a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, Shugaban RTEAN, Musa Maitakobi ya umarcesu da su daina karya doka da oda da kuma kiyayewa a yayin gudanar da ayyukansu. Ya ƙara…
Read More
Kwastom ta kama bindigogin da aka yi safararsu ta ɓarauniyar hanya a Legas

Kwastom ta kama bindigogin da aka yi safararsu ta ɓarauniyar hanya a Legas

Daga BASHIR ISAH Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Ƙasa (NCS) da ke Tin-Can Island a Legas, ta kama bindigogi da sauran kayayyakin da ake zargin wasu ɓata-gari sun shigo da su ta haramtacciyar hanya. Majiyarmu ta ce sauran kayayyakin sun haɗa da rigunan sojoji haɗi da miyagun ƙwayoyi. An ce Kwastom ta kama kayayyakin ne yayin da take duba kayayyakin da aka shigo da su daga ƙetare a tashar jirgin ruwa na Tin-can. Sai dai babu cikakken bayani a kan ko an samu kama wani ko wasu da ke da alaƙa da kayayyakin. Kama kayan na zuwa ne watanni takwas…
Read More
Atiku, Yari da Ningi suna yunƙurin kafa sabuwar jam’iyyar siyasa

Atiku, Yari da Ningi suna yunƙurin kafa sabuwar jam’iyyar siyasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A cikin makon nan ne dai jaridar The Nation ta samu labarin cewa 'yan adawa na shirin kafa sabuwar jam’iyyar da za ta tunkari jam’iyyar APC mai mulki a babban zaɓe mai zuwa. Gabanin shekarar 2027, majiyoyi sun ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zacen shekarar da ta gabata, Alhaji Atiku Abubakar, ya ƙaddamar da ƙudirin jam’iyyar da ake son a yi tare da haɗin gwiwar wasu 'yan majalisar dokokin ƙasar. An tattaro cewa, sansanin Atiku na taka-tsan-tsan da rashin haɗin kan da ke cikin babbar jam’iyyar adawa, yana tunanin cewa idan ta…
Read More
Yadda Tinubu ya dakatar da shirin bada lamuni ga ɗalibai

Yadda Tinubu ya dakatar da shirin bada lamuni ga ɗalibai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An ɗage ƙaddamar da shirin bayar da lamuni ga ɗaliban Nijeriya wanda aka shirya fara shi a gwamnatin Bola Tinubu, sa'o'i 48 gabanin ƙaddamarwa. Akintunde Sawyer, Babban Sakataren Hukumar Kula da Lamuni ta Ilimi ta Nijeriya (NELFUND) ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na AriseTV a ranar Talata. Tun da farko an shirya farawa shirin ne a ranar Alhamis, amma an sake jingine ƙaddamar da shi, yayin da ake yin gyare-gyare don tabbatar da shirin cikin inganci ba tare da wata matsala ba, a cewar Sawyer.  "Ba zan iya…
Read More
Ɗaliban Kuriga: Tinubu ya ƙi amincewa da tayin Sheikh Gumi na tattaunawa

Ɗaliban Kuriga: Tinubu ya ƙi amincewa da tayin Sheikh Gumi na tattaunawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya ƙi amincewa da tayin Sheikh Gumi na tattaunawa da ‘yan bindiga kamar yadda ya umurci hukumomin tsaro a ƙasar nan da su tabbatar an dawo da duk waɗanda aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na ƙasar nan. Idan dai za a iya tunawa, an samu ƙaruwar satar mutane musamman a yankin Arewa maso Yamma na qasar nan a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, inda lamarin neman kuɗin fansa ke ƙaruwa. Wasu gungun masu garkuwa da mutane da suka yi garkuwa da mutane 16 a yankin Gonin-Gora da…
Read More
’Yar’Adua ya zama sabon shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewa

’Yar’Adua ya zama sabon shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Sanata mai wakiltar Katsina ta Tsakiya a Majalisar Dokokin Nijeriya, Abdulaziz Musa Yar’Adua, ya zama sabon Shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewa. An naɗa ’Yar’Adua, ɗan majalisa na jam’iyyar APC, a matsayin sabon shugaban ƙungiyar kwanaki biyu bayan dakatar da Sanata Abdul Ningi. Ningi, mai wakiltar Bauchi ta tsakiya, ya zargi babban zauren majalisar da karkatar da kasafin kuɗin shekarar 2024 har na naira tiriliyan 3.7. Duk da cewa batun ƙara kasafin kuɗi ba sabon abu ba ne a Nijeriya, amma wannan ne karon farko da wani ɗan majalisar dattawa da ya taka rawar gani wajen zartar da…
Read More
Gwamna Lawal ya biya ma’aikatan Zamfara kuɗin hutu

Gwamna Lawal ya biya ma’aikatan Zamfara kuɗin hutu

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Dauda Lawal na jihar Zamfara ya amince kan a biya ma'aikatan jihar kuɗin hutu domin ba su damar yin walwala a cikin watan Ramadan. Mai magana da yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya ce tuni ma'aikatan jihar suka fara samun biya a Larabar wannan makon. Sanarwar manema labarai da Sulaiman ya fitar ta ce, kuɗin hutun kashi 10 cikin 100 ne na albashin da ma'aikaci ke ɗauka a shekara. Sanarwar ta ƙara da cewa, tun bayan da Lawal ya karɓi ragamar mulkin jihar, gwamnatinsa ta ɗauki lamarin walwalar ma'aikatan jihar da wasa ba. Don kuwa, “Ya…
Read More
Tsaro: Lawal ya rattaɓa hannu kan wasu sabbin dokoki

Tsaro: Lawal ya rattaɓa hannu kan wasu sabbin dokoki

Daga BASHIR ISAH Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya rattaba hannu kan wasu sabbin dokoki da suka haɗa da doka haramta amfani da gilashin mota mai duhu da sayar da burodi mara ɗauke da shaida. Sauran hanin sun haɗa da ɗura burodi a buhu da kuma saida fetur sama da lita 50 a lokaci guda ga abubuwan hawa. A ranar Talata Gwamna Lawal ya sanya wa dokokon hannu don su fara aiki a jihar. Kakakin Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya ce doka mai lamba 02 da mai lamba 04, 2024, za su taimaka wajen daƙile abubuwan da suke haifar…
Read More