13
Mar
*Ta janye mata ragowar takunkumai Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bada umarnin gaggawa kan sake buɗe iyakokin Nijeriya da Nijar ta ƙasa da sama, tare da ɗage sauran takunkuman da aka ƙaƙaba wa ƙasar. Mai magana da yawun Shugaba Ƙasa, Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka a ranar Laraba. Sanarwar ta ce hakan ya yi daidai da umarnin ECOWAS wanda ta bayar yayin taron da ta yi ranar 24 ga Fabrairu a Abuja. A cewar sanarwar, “Shugabanni ECOWAS sun amince a kan janye takunkuman da aka kafa wa Jamhuriyyar Nijar, Mali, Burkina Faso da kuma Guinea. “Shugaban Ƙasa ya ba…
