29
Sep
Daga BASHIR ISAH Gawamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 3 ga Oktoban 2022, a matsayin ranar hutu don bikin cikar Nijeriya shekara 62 da samun 'yancin kai. Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya fitar a ranar Laraba mai ɗauke da sa hannun Babban Sakataren Ma'aikatar, Shuaib Belgore. Minista Aregbesola ya yi amfani da wannan dama wajen taya 'yan ƙasa murnar bikin, ya kuma ba su tabbacin gwamnati za ta ci gaba da yin bakin ƙoƙarinta wajen shawo kan matsalolin da suka addabi kasa tare da kyautata rayuwar al'umma. Ya ce, "Duniya…
