02
Oct
Daga BASHIR ISAH Uwargidar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, ta roƙi 'yan Nijeriya su yafe wa Shugaba Muhammadu Buhari kan tsadar rayuwa da matsalolin tsaron da suke fuskanta ƙarƙashin gwamnatinsa. Ta ce, "Mai yiwuwa mulkin bai zama kamili ba, amma ina amfani da wannan dama wajen roƙon yafiyar malamai da da ma al'ummar Nijeriya baki ɗaya. Akwai buƙatar mu haɗa hannu mu yi aiki tare don samun ingantacciyar Nijeriya. Aisha ta yi waɗannan kalaman ne yayin addu'o'i na musamman da aka yi wa Nijeriya yayin sallar Juma'a a ranar Juma'ar da ta gabata albarkacin cikar ƙasar shekara 62 da samun 'yan…
