Labarai

SSS ta buƙaci ASUU ta janye yajin aiki saboda matsalar tsaro

SSS ta buƙaci ASUU ta janye yajin aiki saboda matsalar tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A jiya Alhamis ne hukumar tsaro ta farin kaya, SSS, ta roƙi Ƙungiyar Malaman Jami’o’i, (ASUU) da ta janye yajin aikin da ta shiga, saboda taɓarɓarewar tsaro. Daraktan ma’aikata mai kula da jihar Yobe, Yunusa Abdulkadir, ne ya yi wannan roqo a Damaturu a wajen taron kwata-kwata na uku na daraktocin tsaro na jiha a shiyyar Arewa maso Gabas. Ya ce, yajin aikin da ya gurgunta ilimin jami’o’i a ƙasar, wanda hakan yana da illa ga tsaron ƙasa sakamakon barin matasa a zube babu abin yi. “Kamar yadda muka san ASUU na bin wata…
Read More
Gwamnatin Tarayya za ta karrama Sarkin Zazzau da lambar yabo

Gwamnatin Tarayya za ta karrama Sarkin Zazzau da lambar yabo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ganin irin yadda Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, ya ke jajircewa kan al'amuran da suka shafi al'ummar Nijeriya, Ma'aikatar Ayyuka na Musamman da Al'amuran Gwamnati, za ta karrama shi da lambar yabo a matsayin Kwamandan Oda na Tarayyar Nijeriya. Ministan Ayyuka na Musamman da Al'amuran Gwamnati, Sanata Gorge Akume, ne ya fitar da wannan sanarwar kuma ya rabawa manema labarai a Abuja. Sanarwar ta ce, “ina da farin cikin sanar da ka kai cewa Shugaban ƙasa Muhammadu Buharl, ya amince da ba ka lambar yabo ta ƙasa, a matsayin Kwamandan Oda na Tarayyar…
Read More
An naɗa Malagi Darakta a kwamitin kamfen shugaban ƙasa na APC

An naɗa Malagi Darakta a kwamitin kamfen shugaban ƙasa na APC

Daga WAKILINMU An naɗa mawallafin jaridun Blueprint da Manhaja, Alhaji Mohammed Idris (Malagi), a matsayin Daraktan Sadarwa na Kwamitin Shugaban Ƙasa (PCC) na Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu/Shettima ƙarƙashin Jam’iyyar APC. Naɗin na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai mai ɗauke da sa hannun Sakataren Kwamitin, Rt. Hon. James Abiodun Faleke, wanda jami’yyar ta fitar a ranar Juma’ar da ta gabata. Kwamitin mai mambobi 422, na gudana ne ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin mataimakinsa. An zaɓi Alhaji Mohammed Idris Malagi, tsohon ɗan takarar gwamnan APC a jihar Neja,…
Read More
An yi kira ga matafiya da su guji hawa motoci a kan hanya yayin tafiye-tafiye

An yi kira ga matafiya da su guji hawa motoci a kan hanya yayin tafiye-tafiye

Daga LAWAN MUSA a Bauchi Shugaban tashar motocin da ke Awala ɓangaren 'retain', Malam Auwal Isah Ibrahim, ya yi kira ga matafiya da su ƙaurace wa al'adar nan ta zuwa bakin hanya su tare mota su hau, domin tsira da rayuwarsu. Ya yi wannan kira ne a ofishinsa dake tashar motocin Awala Bauchi, makon da ya gabata. Da farko ya gode wa Allah game da irin nasarorin da suka samu, "musamman haɗin kai da muka samu, bisa jagorancin tsohon shugabanmu Kwamared Abdullahi B. Muhammad, da Alhaji Isma'il Babawo, suka haɗa kai suka samar da haɗin kai a tsakanin mu, 'yan…
Read More
Kisan Ummita: Kotu ta tura Mista Geng zaman gidan yari

Kisan Ummita: Kotu ta tura Mista Geng zaman gidan yari

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Kotun Majistare mai lamba 30 ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Hanif Sanusi Ciroma ta aike da ɗan ƙasar Sin ɗin nan Mista Geng zuwa gidan ajiya da gyaran hali sakamakon rashin hurumin da ta ke da shi na sauraron shari’arsa. Yayin zaman kotun na ranar Laraba da ta gabata, lauyan gwamnati kuma mai gabatar da ƙara Barista Khalifa Auwal Hashim ya roƙi kotu da ta mayar da wanda ake tuhuma gidan gyaran hali a ajiye shi har sai an samu shawarwarin ma'aikarar sharia sakamakon cewar kotun ba ta da hurumi. Ana zargin Mista Geng Qwarong da…
Read More
Gwamnatin Nijeriya na shirin yin dokar da za ta hana cin ganda a faɗin ƙasar

Gwamnatin Nijeriya na shirin yin dokar da za ta hana cin ganda a faɗin ƙasar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa tana nan tana shirin ƙirƙoro da wata doka da za ta hana cin ganda a faɗin ƙasar Darakta Janar na Cibiyar Fasahar Kimiyya da Sarrafa Fatun Dabbobi, NILEST, Muhammad Yakubu ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja. Ya ce dokar ta zamo dole domin a farfaɗo da harkar sarrafa fata a faɗin ƙasar nan. Ya ce za a yi dokar ne domin farfaɗo da kamfanunuwan sarrafa fata a ƙasar nan. A cewarsa, dole ne gwamnati ta hana cin ganda, wacce ba ta da wani amfani wajen gina…
Read More
‘Yan Arewa mazauna Legas sun yi zanga-zangar ƙin jinin kwamishina da sunan Arewa

‘Yan Arewa mazauna Legas sun yi zanga-zangar ƙin jinin kwamishina da sunan Arewa

Daga JAMIL GULMA a Legas Ƙungiyoyin 'Yan Arewa Mazauna Birnin Ikko, sun aiwatar da wata zanga-zangar lumana bisa ga ƙin jinin Arc. Kabiru Ahmed wanda ke riƙe da muƙamin kwamishina a madadin 'yan Arewacin ƙasar nan mazauna Legas. Alhaji Ado Ɗansudu wanda yana daga cikin waɗanda suka gabatar da jawabai ya bayyana cewa ba shakka Arc. Kabiru Ahmed yana ci da gumin 'yan Arewa mazauna Legas saboda bayan ayyana kansa a matsayin shugaba wanda sam ba haka ba ne saboda ba ya tare da kowa, bayan wannan yana yi wa 'yan Arewa zagon ƙasa ta hanyar zaman wuƙa da nama…
Read More
Dubun matar da ke safarar yara daga Kano zuwa Kudancin Nijeriya ta cika

Dubun matar da ke safarar yara daga Kano zuwa Kudancin Nijeriya ta cika

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta ce ta kama wata mata a jihar da ta ɗauko yara tara a motar ɗaukar kaya, daga ƙaramar hukumar Ɗanbatta da ke Kano, ta nufi Jihar Ogun da su. Yaran dai sun haɗa da masu shekaru 10 zuwa 15, kuma matar ta nufi garin Ijebu-Ode da je jihar Ogun ne da su, kafin a tare ta a jihar ta Kaduna. Kakakin rundunar a Kaduna, DSP Muhammad Jalige, ya ce sun tare motar ce a shingen bincike na Kurmin Mashi, bayan sun lura babu taga ko ɗaya a jikinta,…
Read More
‘Yan Chana mazauna Kano sun yi Allah wadai da kisan da ɗan ƙasar su ya yi wa Ummita

‘Yan Chana mazauna Kano sun yi Allah wadai da kisan da ɗan ƙasar su ya yi wa Ummita

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano Ƙungiyar 'Yan Kasuwa ta Al'ummar Sin mazauna Kano ta yi tir da kisan gillar da ɗan asalin ƙasar Sin ya yi wa Ummukulthum Buhari a ranar Juma'ar da ta gabata a gidan iyayenta da ke Unguwar Jan-bulo, ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano. Wannan sanarwar na ƙunshe ne cikin takardar bayani da ke ɗauke da sa hannun mataimakin wakilin mutanen Sin mazauna Kano, Guang Lei Zhang, ta yi nuni da cewa Sinawa mazauna Kano bisa jagorancin Mista Mike Zhang ta yi tir da kisan gillar da ɗan asalin ƙasar Sin, Geng Quanhong ya yi…
Read More
Dodanni sun kai hari coci, sun yi wa fasto dukan tsiya a Filato

Dodanni sun kai hari coci, sun yi wa fasto dukan tsiya a Filato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu gungun matsafa da ake yi wa laƙabi da Dodanni, sun kai hari wani coci a Jihar Filato, inda suka tarwatsa gungun masu ibada, tare da yi wa faston dukan kawo wuqa. Kamar yadda Jaridar Vanguard ta ruwaito, matsafan sun kai harin ne ranar Lahadi a yankin Shikal da ke Ƙaramar Hukumar Langtang ta Kudu a Jihar Filato a daidai lokacin da mabiya ke ibada. Maharan sun lalata kayayyakin cocin, kamar su ganguna da kayan waƙoƙi, tare da tarwatsa mabiya da suka taru suna gudanar da sujuda a cikin cocin. Rahotanni sun tabbatar da…
Read More