Labarai

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane takwas a Katsina

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane takwas a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Waɗansu mutane akan babura da ake kyautata zaton masu satar mutane ne don neman kuɗin fansa sun kutsa kai cikin birnin Katsina a wata unguwa mai suna Shola takwas inda su ka sace mutane 8 ciki hadda matar aure da yarta mai kimanin shekaru biyu. Ɓarayin waɗanda su ka yi dirar mikiya a unguwar mai maƙotaka da babban asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya sun yi ta harba bindigar AK47 tare da valle ƙofofin gidajen mazauna unguwar domin samun damar shiga daga ciki don aiwatar da ta'addanci. Wata Binta Abdulmumin ta bayyana wa majiyar Manhaja yadda…
Read More
Mun kashe Naira biliyan bakwai don samar da ingantaccen ilimi – Gwamnatin Kano

Mun kashe Naira biliyan bakwai don samar da ingantaccen ilimi – Gwamnatin Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Kano ta ce a wani ɓangare na sauke nauyin tabbatar da ingantacciyar hanyar koyo da koyarwa a makarantu, ta kashe Naira biliyan bakwai. Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana haka a ranar Talata yayin da ya buɗe taron zangon shekara na biyu da Hukumar Ilimin Bai-ɗaya, UBEC tare da shugabannin zartaswa na SUBEB na ƙasa a ɗakin taro na Africa House da ke gidan gwamnatin Kano. Ganduje ya bayyana cewa, magance ƙalubalen da ke tattare da matsalar rashin zuwan yara makarantu, na ɗaya daga cikin abin da ya sanya jihar Kano…
Read More
‘Yan majalisu sun nemi a maida murafun magudanan ruwa na titin birnin Abuja

‘Yan majalisu sun nemi a maida murafun magudanan ruwa na titin birnin Abuja

Daga AMINA YUSUF ALI Majalisar wakilan Nijeriya ta yi kira ga hukumar gudanarwa ta birnin Tarayyar Abuja (FCTA) da ta gaggauta rufe dukkan ramukan saman magudanan ruwa na titi waɗanda suke a buɗe. Domin a cewar su, barin su haka yana jawo asarar rayuka da dukiyoyin al'umma. Wannan kiran da 'yan majalisar suka yi ya biyo bayan amincewa da wani ƙuduri da ɗan majalisa, Musa Pali (APC Bauci) ya gabatar a zauren Majalisar a ranar Asabar ɗin da ta gabata a Abuja. Shi dai ramin saman magudanan ruwa wani rami ne da ake yinsa a saman magudanan ruwa ta yadda…
Read More
2023: Okowa ya zama abokin takarar Atiku a PDP

2023: Okowa ya zama abokin takarar Atiku a PDP

Daga BASHIR ISAH Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ba da sanarwar ɗaukar Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa. Wannan na zuwa ne yayin da ya rage ƙasa da sa'o'i 24 kafin cikar wa'adin hukumar zaɓe INEC, kan kowace jam'iyya ta tabbatar da ta miƙa sunayen 'yan takararta na zaɓen 2023 kada ya wuce Juma'a, 17 ga Yuni. Atiku ya ba da sanarwar haka ne ranar Alhamis a babban ofishin PDP da ke Abuja. Ya jaddada cewa haɗin kan jam'iyya na da matuƙar muhimmanci muddin suna son lashe zaɓen 2023, don haka ya…
Read More
Rubutun adabin bariki ya gurɓata tarbiyyar yara da dama – Maman Amatullah

Rubutun adabin bariki ya gurɓata tarbiyyar yara da dama – Maman Amatullah

“Muna samun nasarar yaƙi da yaɗuwar rubutun batsa” Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A sakamakon yadda ake kokawa da cigaba da ƙaruwar marubuta labaran batsa a tsakanin marubutan adabi, waɗanda ake kira da marubuta adabin bariki, wasu marubuta sun yunƙuro domin wayar da kan marubuta da kawo sauyi a harkar rubutun adabi. Saboda haka suka kafa ƙungiyar Jarumai Writers Association, don nuna halin jarumta da jajircewa wajen nuna halayen ƙwarai da kyautata tarbiyyar matasa maza da mata ta hanyar rubuce rubucen su. Khadija Salis Ibrahim da aka fi sani da Maman Amatullah na cikin sahun gaba a wannan gangami na yaƙi…
Read More
2023: Ina da yaƙinin APC za ta lashe zaɓe – Adamu

2023: Ina da yaƙinin APC za ta lashe zaɓe – Adamu

Daga BASHIR ISAH Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya ce, APC na da yaƙinin za ta lashe zaɓen 2023 wanda zai gudana cikin aminci da adalci. Adamu ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Jadiyar Poland a Nijeriya, Joanna Tarnawska, a ofishinsada ke Abuja. Ya ce, duba da irin goyon bayan ɗimbin ‘yan Nijeriya da APC ke da shi, babu yadda za a yi jam’iyyar ta sha kaye a zaɓen 2023. Jakadiyar ta ziyarci Adamun ne bayan da jam’iyyarsa ta kammala zaɓen fidda gwani cikin nasara innda ta zabi dan takarar da zai yi…
Read More
Da ɗumi-ɗuminsa: Buhari zai ziyarci Kano gobe

Da ɗumi-ɗuminsa: Buhari zai ziyarci Kano gobe

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, zai kai ziyara Jihar Kano a gobe Alhamis, 16 ga watan Yuni, 2022. Hakan na cikin saƙon da mai taimaka wa Shugaban Ƙasar kan sabbin kafafen sadarwa, Malam Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a yau Laraba. Bashir Ahmad ya ce, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai je Jihar Kano ne domin halartar taron bikin yaye sabbabbin jami’an 'yan sanda a Kwalejin Horas da 'Yan Sandan da ke garin Wudil a jihar.
Read More
’Yan sanda sun fatattaki ’yan bindiga a hanyar Kaduna zuwa Abuja

’Yan sanda sun fatattaki ’yan bindiga a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Haɗaɗɗiyar tawagar ’yan sanda da sojoji sun daƙile wani shiri da ’yan bindiga suka yi a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Litinin. Rundunar ta kashe ɗaya daga cikin ’yan bindigar, inda ta ƙwato bindiga ƙirar AK47 guda ɗaya da kuma babura guda tara. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna. Ya bayyana cewa, wannan matakin wata alama ce ta samun nasara da kuma manufa ta haɗin gwiwa tsakanin ’yan sanda da sojoji a jihar Kaduna. “A ranar Litinin, 13…
Read More
An tsaurara matakan tsaro yayin rantsar da zaɓaɓɓun Ciyamomi da kansiloli a Abuja

An tsaurara matakan tsaro yayin rantsar da zaɓaɓɓun Ciyamomi da kansiloli a Abuja

Daga AMINA YUSUF ALI An tsaurara matakan tsaro ainun a garin Abuja a yayin da sabbin zaɓaɓɓun Ciyamomi da Kansiloli suke amsar rantsuwar kama aiki. Ministan Birnin Tarayyar Abuja, Muhammad Musa Bello shi ne ya jagoranci taron ƙaddamar da rantsuwar sababbin shugabannin ƙananan hukumomi da Kansiloli na gundumoni shida da suke garin Abuja. Wannan taro da aka daɗe ana dako ya faru ne a cibiyar fasaha da al'adu ta Cyprian Ekwensi wacce take a unguwar Area 10, Garki a garin Abuja. An tsaurara matakan tsaro sosai a yayin gudanar da taron. Wakilin jaridar Blueprint ya samu yin tozali da zaɓaɓɓen…
Read More
2023: Buhari ya sake ganawa da gwamnonin APC

2023: Buhari ya sake ganawa da gwamnonin APC

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi ganawar sirri tare da gwamnonin APC ranar Talata a Fadarsa da ke Abuja domin tattauna batun wanda zai zame wa Tinubu mataimaki a babban zaɓen 2023. Gwamnonin sun iyarci Buharin ne ƙarƙashin ƙungiyarsu ta Progressive Governors' Forum (PGF), ƙarƙashin jagorancin Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi. Bayanan da Manhaja ta kalato sun ce, mahalarta taron sun haɗa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari, Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha, Gwamna Babagana Zulum na Borno, Nasir El-Rufai na Kaduna, Mohammed Badaru Abubakar na Jigawa, Abdullahi Sule na Nasarawa, Simon…
Read More