Labarai

Yajin Aiki: Gwamnati, ASUU da daginta sun koma teburin sulhu

Yajin Aiki: Gwamnati, ASUU da daginta sun koma teburin sulhu

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta koma teburin sulhu don ci gaba da tattaunawa tsakaninta da ma'aikatan jami'o'in Nijeriya. Jaridar Punch ta ruwaito cewa, kamata ya yi kwamitin sulhun da gwamnatin ta kafa a ce ya kammala aikin sulhunta tsakanin ɓangarorin da lamarin ya shafa tun a ranar 7 ga Yuni, 2022 amma hakan bai yiwu ba. Sai dai, sahihan bayanai sun tabbatar cewa ɓangaaren ƙungiyoyin da lamarin ya shafa zai gana da gwamnati a wannan Litinin ɗin, yayin da wani sashen zai gana da Gwamnatin a Juma'a mai zuwa. Wata majiya ta kusa da ASUU ta ce, "Za mu…
Read More
Masu sayar da GSM na Zamfara sun tabbatar da sace mutanensu 30 da ‘yan bindiga suka yi

Masu sayar da GSM na Zamfara sun tabbatar da sace mutanensu 30 da ‘yan bindiga suka yi

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ƙungiyar masu sayar da wayoyin hannu ta Jihar Zamfara ta tabbatar da cewa, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mambobinsu kimanin 30. Shugaban ƙungiyar, Comrade Kabir Garba Muktar ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Gusau a ranar Lahadi. A cewarsa, an yi garkuwa da mambobinsu ne a tsakanin Turata zuwa Lambar Bakura a hanyarsu ta komawa Gusau yayin da suka halarci bikin auren abokinsu a Ƙaramar Hukumar Tambuwal ta jihar Sakkwato ranar Asabar. "‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mambobinmu sama da 50 da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin ranar Asabar…
Read More
Za mu kashe Naira biliyan biyu kan tantance ma’aikatan makarantu – UBEC

Za mu kashe Naira biliyan biyu kan tantance ma’aikatan makarantu – UBEC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Kula da Makarantu a Matakin Farko (UBEC) ta ce, za ta kashe Naira biliyan biyu wajen tantance malaman makarantu a cikin kwana 10. Babban Sakataren Hukumar UBEC, Hamid Bobboyi, ya ce, an ware kuɗaɗen ne domin tantance ma’aikatan makarantun a faɗin Nijeriya a shekarar 2022 da muke ciki. Ya ce, hukumar za ta tantance makarantu a jihoi 17 na yankin Kudu da yankin Arewa mai jihohi 19 da kuma Birnin Tarayya, Abuja, daga ranar 4 zuwa 23 ga watan Yuli mai mkamawa. Bobboyi ya shaida wa taron tantance ma’aikata da ya gudana a Abuja, inda…
Read More
Rundunar ’yan sandan Katsina ta bai wa iyalan jami’anta tallafin kuɗi

Rundunar ’yan sandan Katsina ta bai wa iyalan jami’anta tallafin kuɗi

Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar 'yan sandan Jihar Katsina ta raba wa iyalai da magadan jami'anta da suka rasa rayukansu lokacin gudanar da ayyukansu cakin kuɗi na Naira Milyan 53 da dubu ɗari tara. Da ya ke miƙa cakin kuɗin ga iyalai da  magadan 'yan sandan su 25  a hedikwatar rundunar kwamishinan 'yan sandan jihar Katsina Idris Dauda Dabban ya bayyana cewar bada cakin kuɗin wata Inshora ce da babban sufeto janar na 'yan sanda Alƙali Baba ya ƙirƙiro da shi don tallafawa iyalan jami'an da su ka rasu lokacin gudanar da aiyukansu. Ya ci gaba da cewa, an…
Read More
Sarkin Kwatarkwashi Alhaji Ahmad Umar, Basarake mafi daɗewa a Zamfara ya rasu

Sarkin Kwatarkwashi Alhaji Ahmad Umar, Basarake mafi daɗewa a Zamfara ya rasu

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Sarkin gargajiya mafi daɗewa a Jihar Zamfara, Sarkin Kwatarkwashi, Alhaji Ahmad Umar, ya rasu Alhamis da ta gabata. A cewar sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Balarabe Danisa, ga manema labarai cewa, sarkin ya rasu ne bayan gajeriwar jinya yana da shekaru 93 a duniya. Marigayi Alhaji Ahmad Umar ya kasance basaraken gargajiya mafi daɗewa kuma babba akan karagar mulki ba a Zamfara kaɗai ba, har ma a faɗin Nijeriya bakiɗaya, inda ya kwashe shekaru 61 a matsayin Sarkin Kwatarkwashi. Sarkin mai shekaru 93, an fara naɗa shi hakimin ƙauye a…
Read More
Harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna: ‘Yan bindiga sun sako mutum 11 da ke hannusu

Harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna: ‘Yan bindiga sun sako mutum 11 da ke hannusu

Daga BASHIR ISAH 'Yan bindiga sun sako fasinjojin da suka yi garkuwa da su a harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna a lokutan baya. Hakan ya biyo bayan sasantawar da aka yi ne tsakanin Gwamnatin Tarayya da 'yan bindigar. Ɗan jarida na kusa Sheikh Ahmad Gumi, Malam Tukur Mamu ya bayyana cewa, mutum 11 da lamarin ya shafa ne 'yan bindigar suka sako su a ranar Asabar. Ya ce, an kwashi waɗanda aka sakon baki ɗayansu zuwa Abuja don duba lafiyarsu a bisa umarnin Shugan Ƙasa Muhammadu Buhari kafin daga bisani a haɗa su da 'yan uwansu. Mamu ya ƙara…
Read More
Samar da tsaro babu wutar lantarki a Nijeriya almara ce – Alhaji Ashiru Gezawa

Samar da tsaro babu wutar lantarki a Nijeriya almara ce – Alhaji Ashiru Gezawa

Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano An bayyana cewa duk wani shugaba da zai zo nan gaba a Nijeriya koma na yanzu da ya ce zai inganta tsaro da tattalin arziƙi da duk wani cigaba ba tare da ya samar da wadataccen hasken wutar lantarki ba a Nijeriya to abu ne da ba zai yiwu ba kuma almara ce ko kuma yaudara. Wannan jawabin ya fito ne daga bakin Alhaji Ashiru Ali Muhammad Yammusa Gezawa, Shatiman Sardaunan Alagwado a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Alhamis ɗin makon jiya. Har wa yau, Yammusa Gezawa ya ƙara…
Read More
Babu wanda ya taimaka wa Shugaba Buhari yayin da aka rufe kan iyakokin ƙasa – Uba Yakasai

Babu wanda ya taimaka wa Shugaba Buhari yayin da aka rufe kan iyakokin ƙasa – Uba Yakasai

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano Dangane da buɗe iyakokin ƙasa da Gwamnatin Tarayya ta yi kwanakin baya, Alhaji Uba Zubairu Yakaisa, wanda shi ne shugaban kasuwannin Sabongari, Singa da Galadima da ke Kano, ya bayyana cewa babu wanda ya taimaka wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari don ganin an samu gagarumar nasarar kulle iyakokin, musamman wajen bunƙasa harkar noma. Yakasai ya kuma bayyana cewa, "ba batun ɓoye-ɓoye manyan 'yan kasuwar da suke iƙirarin cewa za su taimaki Maigirma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yayin rufe waɗannan iyakoki lokacin baya ba su ba shi goyon baya ba wajen abinda suka ɗauka a…
Read More
Ban ce a ƙirƙiro ma’aikatar ɓarayin daji ba – Sheikh Gumi

Ban ce a ƙirƙiro ma’aikatar ɓarayin daji ba – Sheikh Gumi

Daga WAKILINMU Fitaccen malamin addinin Musulunci na Nijeriya, Sheikh Ahmad Gumi ya yi ƙarin haske kan shawarar da ya bayar ta buƙatar a samar da ma’aikatar kula da harakokin makiyaya a Nijeriya. Yayin zantawa da manema labarai a wani bikin nuna al’adun Fulani a Abuja, Shehin Malamin ya ce wasu kafofin yaɗa labarai sun sauya abin da ya faɗa yana mai ƙaryata rahotannin da ke cewa ya ce “ya kamata gwamnati ta ƙirƙiro ma’aikatar ɓarayin daji.” “Sun mayar da makiyaya a matsayin 'yan fashin daji,” kamar yadda malamin ya bayyana a wani bidiyo da kafar talabijin ta Channels ta wallafa…
Read More
Kimanin mutane miliyan 1.5 ne suka samu rigakafin Korona a Jihar Zamfara

Kimanin mutane miliyan 1.5 ne suka samu rigakafin Korona a Jihar Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Kimanin mutane miliyan aƙalla miliyan ɗaya da rabi ne suka samu rigakafin Korona a Jihar Zamfara. Manajan shirin na hukumar kula da lafiya ta Jihar Zamfara, Mustafa Aliyu ne ya bayyana haka yayin da yake gabatar da kasida a taron bita na yini ɗaya da hukumar ta shirya wa ‘yan jarida a jihar a ranar Talata. Ya bayyana cewa, mutane 853,392 ne suka samu allurar farko, mutane 555,509 kuma sun karɓi kashi na biyu, yayin da mutane 107,209 suka samu maganin ƙara kuzari. Aliyu ya ce da wannan ci gaban, kashi 33 na al’ummar jihar…
Read More