11
Jan
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar sojojin Nijeriya ta rufe kasuwar shanu ta Song bayan bayanan sirri sun nuna cewa, ’yan Boko Haram na hada-hadar kasuwancinta a kasuwar. Rufe kasuwar dai ya haifar da ce-ce-ku-ce, yayin da wasu ’yan kasuwar ke zargin matakin da sojoji suka ɗauka, bayan da suka ƙi amincewa da buƙatar sojojin da ke wurin na neman maƙudan kuɗaɗe domin su samu damar yin kasuwanci. Wani ɗan kasuwa da ya zanta da manema labarai, ya ce, sojojin sun buƙaci ƙungiyar ’yan kasuwa da ke kula da kasuwar da ta ba su miliyoyin naira. Amma Kwamandan Birgediya 23, Gibson…
