22
Feb
Daga WAKILIN MU A wannan Litinin ne Ƙasar New Zealand ke cika sheka 10 da faruwar ibtila'in girgizar ƙasa da ya auku a birnin Christchurch wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 185, tare da jikkata wasu dubbai. Girgizar ƙasar wadda ta kai ƙarfin maki 6.3 da zurfin kilomita 5, ta faru ne a ranar 22, Fabrairu, 2011. Domin tuna zagayowar wannan rana, ɗaruruwan 'yan ƙasar ne suka taru a wani wajen taro a birnin Christchurch domin tunawa da duka waɗanda suka rasa rayukansu a wancan lokaci. Haka nan, an ga yadda aka yi ƙasa-ƙasa da tutoci a sassan ƙasar domin…