03
Feb
Daga WAKILIN MU 'Yan jam'iyyar National League for Democracy a ƙasar Myanmar, sun yi kira da a sako Aung San Suu Kyi tare da sauran jagororinsu da aka tsare a Talatar da ta gabata. Suna masu bayyana juyin mulkin da sojojin ƙasar suka yi a ƙasar a matsayin al'amari da ya yi wa tarihin sojin ƙasar tabo mara kyau. Da sanyin safiyar Litinin da ta gabata sojoji suka kama Suu Kyi da ta kasance shugabar jam'iyyarsu tare da shugaban ƙasar, Win Myint. Bayan juyin mulkin, ba tare da ɓata lokaci ba sojojin suka naɗa wani tsohon janar, Min Aung Hlaing,…