19
Apr
Daga WAKILINMU Nijeriya ta tura gudunmawar 'yan sanda su 144 ya zuwa ƙasar Somaliya domin aikin tallafa wa fannin tsaron ƙasar. Nijeriya ta tura jami'an nata ne ƙarƙashin tawagar AMISOM ta ƙungiyar tarayyar Afirka (AU). Babban jami’in tsare-tsare na tawagar AMISOM a ƙasar, Daniel Ali Gwambal, ya bayyana cewa 30 daga cikin 'yan sandan za su yi aiki na tsawon shekara guda ƙarƙashin tawagar AMISOM, inda za a tura su yankunan Beletweyne da ke jihar HirShabelle, sauran kuma za su yi aiki a sassan birnin Mogadishu babban birnin ƙasar. Jami'in ya ce sauran ‘yan sandan za su yi ayyukan tsaro…