23
Apr
Daga BAMAI ALHAJI DABUWA Sunan Marubuciya: Maryam Abdul. Shekarar Bugu: Babu. ISBN: 978-978-982-968-4. Mai Sharhi: Bamai Dabuwa. Lambar Waya: 07037852514. Gabatarwa/Abubuwan Burgewa: Littafin 'Duhun Damina' littafi ne da aka yi amfani da wani irin salo mai kama da tafiyar kura. Shi ne littafin da ya kawo zunzurutun kuɗi sama da miliyan guda a ranar da aka ƙaddamar da shi. Littafin ya taɓo wata matsala da kusan kowa ke tsoron taɓawa saboda gudun tambayar kai ta ya aka yi ka sani? Wasu kuma hankalinsu bai kai wajen ba, musamman iyaye, amma kuma rayuwar 'ya'yansu ce dumu-dumu a ciki. Littafi ne da…