19
Oct
"Masu hali ba sa ƙarfafa gwiwar marubuta" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Rufa'i Abubakar Adam, wanda aka fi sani da R.A. Adamu, wani matashin marubuci ne da ya taso cikin sha'awar karance-karance da rubuce-rubuce har kafin Allah ya sa ya zama mai aikin ɗab'i da zane-zane a na'urar kwamfuta. Yana daga cikin matasan marubutan da suka kafa ƙungiyar Gamayyar Marubutan Jihar Gombe (GAMJIG), domin haɗa kan marubutan Gombe da samar da wasu hanyoyi na bunƙasa cigaban adabi da harshen Hausa. Gwagwarmayar da ya sha a baya a yayin ƙoƙarinsa na ganin ya zama marubuci ya silar kawo sauyi a Jihar Gombe,…
