Wasanni

Za a ƙaddamar da gasar Super League a Afirika

Za a ƙaddamar da gasar Super League a Afirika

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban hukumar ƙwallon ƙafar Afirika, Patrice Motsepe zai ƙaddamar da gasar Super League ta ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar Afrika, tare da alƙawarin dala miliyan ɗari ga ƙungiyoyin nahiyar. Tun da shugaban hukumar ƙwallon ƙafar duniya, FIFA, Gianni Infantino ya bada shawarar gasar a farkon shekarar 2020 ne ake ta shiri tare da ƙoƙarin tsara gasar, kuma babu irin turjiyar da makamancin wannan yunƙuri ya gamu da shi a Turai cikin shekarar da ta gabata. Ƙungiyar ’yan wasa a Afrika ta Kudu ce kawai ta soki wanna shiri a wata sanarwa da ta fitar a wannan mako, inda…
Read More
An canja jadawalin fara gasar kofin duniya

An canja jadawalin fara gasar kofin duniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Za a fara gasar kofin duniya ranar Lahadi 20 ga watan Nuwamba, inda Ƙatar mai masaukin baƙi za ta kara da Ecuador. Tun farko an tsara karawar rukunin farko ranar 21 da ƙarfe 16:00 agogon GMT, kuma wasan Ƙatar shi ne na uku daga cikin wanda aka tsara yi. An shirya da buɗe gasar da wasa tsakanin Senegal da Netherlands ranar Litinin 22 ga watan Nuwamban. Daga baya FIFA ta karɓi ƙorafi daga hukumar ƙwallon ƙafa ta Kudancin Amurka da ake kira Conmebol, wadda ta ce bisa al'ada ana bikin buɗe gasa ko dai da mai…
Read More
’Yar wasan Nijeriya, Tobi Amusan ta sake kafa tarihi a wasan guje-guje

’Yar wasan Nijeriya, Tobi Amusan ta sake kafa tarihi a wasan guje-guje

Daga MAHDI M. MUHAMMAD ’Yar wasan Nijeriya, Tobi Amusan ta yi nasarar kare kambunta na gasar tseren mita 100 na ƙasashe renon Ingila, wato Commonwealth, bayan da ta kai matakin farko a ranar Lahadi a filin wasa na Alexander da ke Birmingham. ’Yar wasan ta sake kafa sabon tarihi bayan da ta kammala tseren mita 100 cikin daƙiƙa 20 da sakan 30, wanda hakan ya ba ta damar lashe lambar zinare ga ƙasarta Nijeriya. Mai riƙe da kambun gasar ta duniya ta kawo ƙarshen tarihin tseren daƙiƙa 16 da sakan 65 da Brigitte Foster-Hylton ta Jamaica ta kafa a Melbourne,…
Read More
Yadda ’yar Nijeriya, Tobi Amusan ta kafa tahiri a gasar tseren duniya

Yadda ’yar Nijeriya, Tobi Amusan ta kafa tahiri a gasar tseren duniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tobi ’yar gaban goshin Nijeriya ce - BuhariYadda nasarar ta sa ’yan Nijeriya zubar da hawayen farin cikiKocin Super Eagles ya yaba wa Tobi da BrumeAfirika na alfahari da Tobi - Usain BoltShugaban Hukumar AFN ya taya ta murna 'Yan Nijeriya sun yi matuƙar farin cikin ganin yadda Tobi Amusan, 'yar shekara 25, haifaffiyar garin Ijebu Ode na Jihar Ogun, ta zama 'yar wasan Nijeriya ta farko da ta lashe kofin zinare a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya, bayan da ta samu nasara a gasar tseren mita 100 na mata a Oregon da ke ƙasar…
Read More
Dalilin da ya sa Kano Pillars ta faɗi daga Firimiyar Nijeriya a bana

Dalilin da ya sa Kano Pillars ta faɗi daga Firimiyar Nijeriya a bana

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ta tabbata cewar Kano Pillars ta faɗi daga gasar Firimiyar Nijeriya bana a karo na uku a tarihin ƙungiyar. Tun farko ƙungiyar da aka kafa a 1990 ta faɗi daga gasar Firimiyar ƙasar a shekarar 1994 da 1999. Ƙungiyar da ake kira sai masu gida wadda ta lashe kofin babbar gasar tamula ta Nijeriya karo huɗu ba za ta buga kakar da za a yi ta 2022/23 ba. Ƙungiyar tana da daɗaɗɗen tarihi a fagen taka leda a ƙasar da Afirka, wadda ta samar da fitattun 'yan wasa masu magoya baya da yawa. Shugaban marubuta labarin…
Read More
Tarihin da Ahmed Musa ya kafa masu wahalar karyawa a Nijeriya

Tarihin da Ahmed Musa ya kafa masu wahalar karyawa a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ahmed Musa, ya fara buga wa Super Eagles ta Nijeriya wasa ne a ranar 5 ga watan Agustan 2010, inda ya shiga wasan ne a canjin Mikel John Obi, a wasan da suka doke Madagascar da ci 2-0 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin AFCON na shekarar 2012. Ya buga gasar AFCON guda uku (2013, 2019 da 2021). Ya samu nasarar lashe guda daya a cikin 2013 AFCON. Sannan ya buga gasar cin kofin duniya guda biyu (2014 da 2018). Musa shi ne ɗan wasan da ya fi kowa zura ƙwallaye a ragar Nijeriya…
Read More
Jerin ’yan wasan da ke gogayyar zama Gwarzon Ɗan Ƙwallon Afirka na 2022

Jerin ’yan wasan da ke gogayyar zama Gwarzon Ɗan Ƙwallon Afirka na 2022

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka CAF, ta fitar da jerin ’yan wasa goma da ke takarar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na 2022. Za a bayyana gwarzon bana a Rabar a Morocco ranar 21 ga watan Yulin 2022. Cikin goman da Hukumar CAF ta sanar sun haɗa da mai riƙe da kyautar, Sadio Mane (Senegal da Bayern Munich) da wanda ya tava lashe kyautar Riyad Mahrez (Algeria da Manchester City) da Mohamed Salah (Masar da Liverpool). A bana ma dai lamarin bai zo wa Nijeriya da sa’a ba, inda babu ɗan wasan tawagar Super Eagles ko ɗaya da ya samu shiga…
Read More
Christophe Galtier ya zama sabon kocin PSG

Christophe Galtier ya zama sabon kocin PSG

An naɗa Christophe Galtier a matsayin kocin Paris St-Germain bayan tafiyar Mauricio Pochettino. Galtier ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyu daga nan zuwa shekarar 2024. Kocin mai shekaru 55, wanda ya jagoranci Lille ta lashe kofin Ligue 1 a shekarar 2021, shi ne koci na bakwai da PSG ta yi tun bayan da Qatar ta karɓe kulob ɗin a shekarar 2011. Galtier yana ɗaya daga cikin masu horarwa biyu kacal da suka hana PSG lashe gasar Ligue 1 a shekaru goma da suka gabata, tare da Leonardo Jardim na Monaco a 2016-17.
Read More
Shugaban Barcelona ya bayyana makomar manyan ’yan wasan ƙungiyar

Shugaban Barcelona ya bayyana makomar manyan ’yan wasan ƙungiyar

Shugaban Barcelona, Joan Laporta ya bayar da bayani kan halin da Gavi da Ousmane Dembele ke ciki a ƙungiyar. Ya ce, ɗan wasan da kwantiraginsa ya ƙare zai ci gaba da zama yayin da a ƙarshen zai karɓi tayin da ya ke da shi idan yana son cigaba da zama. Da ya ke magana game da Gavi, Laporta ya ce, “Gavi zai cigaba da zama ɗari bisa ɗari tare da Barca, muna da yarjejeniya da shi.” Gavi, mai shekaru 17, ana ɗaukarsa a halin yanzu ɗaya daga cikin samari masu kwarin gwiwa a fagen ƙwallon ƙafa a duniya. Ɗan wasan…
Read More
Kotu ta wanke tsohon shugaban FIFA daga zargin cin hanci

Kotu ta wanke tsohon shugaban FIFA daga zargin cin hanci

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kotu a Switzerland ta wanke tsohon shugaban FIFA Sepp Blatter da mataimakinsa Michael Platini kan zargin cin hanci. Blatter, mai shekara 83, ya bai wa Platini wasu kuɗi da suka kai kimanin Swiss francs miliyan biyu, daidai da fan miliyan 1.5 a ranar 18 ga watan Junairun 2011, bayan mako biyu aka tura kuɗin zuwa asusun Platini daga asusun FIFA. Dukkansu dai sun musanta aikata ba daidai ba, inda suka ce kuɗin da aka biya Platini kuɗi ne na wani aiki da ya yi wa FIFA. Bayan bayyana a gaban a yau Juma'a, Blatter ya ce,…
Read More