CMG ya gabatar da tambarin musamman da kayan murnar bikin bazara na ƙasar Sin na shekarar 2023 mai alamar zomo

Daga CMG HAUSA

A yau ne, babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG ya gabatar da tambarin musamman da kayan murnar bikin bazara na kasar Sin na shekarar 2023 mai alamar zomo, mai suna “Tu Yuan Yuan” a hukumance.

Za a yi amfani da kayayyakin ne a gun bikin murnar ranar bikin bazara mai taken “kara jin dadin zaman rayuwa a kasar Sin a sabon zamani”.

Bayan hakan, an shaida cewa an kusantar da lokacin ranar bikin murnar bikin bazara na CMG na shekarar 2023. Kuma kayayyakin fatan alheri na Tu Yuan Yuan mai salon gargajiya tare da salon zamani zai yi wa masu kallo fatan alheri a ranar bikin, kafin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin.

Mai fassara: Zainab Zhang

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *