Dokar hana kiwo: Ƙungiyar Miyetti Allah ta nemi Majalisar Tarayya ta taka wa gwamnoni birki

Ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore, ta yi kira ga Majalisar Ƙasa da ta sa baki wajen dakatar da yunƙurin da wasu gwamnonin Nijeriya suka yi na neman kafa dokar da za ta hana Fulani makiyaya kiwo a sake.

Sakataren ƙungiyar na ƙasa, Saleh Alhassan, shi ne ya yi wannan kira a wajen wani taro da suka gudanar a garin Uke da ke yankin Ƙaramar Hukumar Karu a jihar Nasarawa.

Alhassan ya ce wannan doka za ta yi wa zaman lafiyar da ake samu yanzu tarnaƙi a ƙauyuka, da yi wa zamantakewa barazana da kuma tsananta matsalar satar shanu.

Ya ci gaba da cewa, samar da wannan doka zai kassara harkar kiwo tare da talauta milyoyin jama’a da suka dogara da harkar dabbobi don iya rayuwa.

Don haka Alhassan ya yi kira ga Majalisar Tarayya da ta taimaka ta shigo cikin wannan al’amari don samun maslaha ta hanyar dubawa tare da yi wa dokar killace wuraren kiwo da majalisar da ta gabata ta ƙirƙiro kwaskwarima sannan a ƙaddamar da ita.

Haka nan, sakataren ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ƙirƙiro Ma’aikatar Kiwon Dabbobi da Kifaye kamar dai yadda ake samu a sauran ƙasashen Afrika.

Ya jaddada buƙatar da ke akwai gwamnati ta gudanar da bincike sannan ta tattara bayanan duka wuraren kiwo da laɓi-laɓin shanu da ake da su domin bunƙasa su ta yadda za a iya samun a ƙalla gandun dajin kiwon dabbobi guda ɗaya a kowace mazaɓar sanata daga mazaɓun da ake da su a faɗin ƙasar nan.

Kazalika, Alhassan, ya yi kira ga gwamnati da ta bai wa Shirin Ilimin ‘Ya’yan Fulani Makiyaya (Nomadic Education) muhimmanci domin inganta shi yadda ya kamata.

Haka nan, Miyetti Allah Kautal Hore ta yi tir da yadda Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ke tafiyar da lamarin Fulani makiyaya a jiharsa, tare da neman sa kan ya bai wa ɗaukacin al’ummar Fulani haƙuri kan haka.

A hannu guda, Alhassan ya ce sun yaba wa Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari dangane da sauraren kiraye-kirayensu game da batun dawo da gandun dazuzzukan kiwon dabbobi da laɓin shanu da kuma samar da wasu sabbi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *