Ekweremadu da matarsa sun faɗa a komar ‘yan sanda a ƙetare

Daga BASHIR ISAH

‘Yan Sanda a birnin London sun tsare tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Dr. Ike Ekweremadu tare da mai ɗakinsa, Beatrice.

A cewar jaridar Sky, an tsare su biyun ne bisa zargin haɗin baki wajen ɗebe sassan jikin wani yaro.

Sai dai, an ce tuni an ɗauki yaron da lamarin ya shafa zuwa wani wuri don ba shi kariya.

Jaridar Sky ta ruwaito cewa, “Ana tuhumar wasu mutum biyu da haɗin baki wajen ɗaukar wani yaro zuwa Birtaniya domin ɗebe wasu sassan jikinsa, in ji ‘yan sanda.

“An tsare Beatrice Nwanneka Ekweremadu, ‘yar shekara 55 da kuma Ike Ekweremadu, mai shekaru 60, kuma za a gurfanar da su a kotun Majistiri da ke Uxbridge yau.

“Ana tuhumar su biyun da suka fito daga Nijeriya ne biyo bayan binciken da ‘yan sanda suka gudanar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *