Fim ɗin ‘Fanan’ ya fito da ni idon duniya – Jaruma Sabira Mukhtar

DAGa MUKHTAR YAKUBU, a Kano

Sabuwar jaruma a masana’antar fina-finan Hausa ta masana’antar Kannywwod, Sabira Mukhtar, tana ɗaya daga cikin jarumai mata da a ke ganin nan gaba kaɗan za ta zamo babbar jaruma, saboda irin rawar da ake ganin ta taka a cikin fim ɗin ‘Fanan’. Duk da cewar ba shi ne fim ɗinta na farko ba, amma dai fim ɗin ‘Fanan’ shi ne ya fito da ita. A cikin tattaunawar su da wakilinmu, jarumar ta yi bayani a kan shigowarta harkar fim, da kuma yadda fim ɗin ‘Fanan’ ya ɗaga darajarta, har ya zamo abin alfahi a gare ta, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance:

MANHAJA: Da farko za mu so ki gabatar da tarihin rayuwarki ga masu karatun mu.
SABIRA MUKHTAR: To ni dai sunana Sabira Mukhtar, kuma ni haifaffiyar garin Kano ce, a nan na tashi, na yi karatun Firamare da Sakandare har zuwa Jami’a.

To, da yake kin ce kin yi karatu har zuwa Jami’a, ko ya aka yi kika samu kanki a cikin masana’antar kannywwod?
To gaskiya na samu shiga harkar fim ne ta dalilin Furodusa Abdul Amat, wanda tun kafin na shigo mu na mutunci da shi, to kuma da zan shigo sai ya zame mini hanya.

Kenan tun kafin ki fito a fim ɗin ‘Fanan’ kin yi wasu fina-finai a baya?
Eh. Gaskiya na yi wasu fina-finan ba shi ba ne na farko, duk da cewar a yanzu ba zan iya kawo su duka ba, amma dai zan iya tunawa, na yi ‘Ranar rabuwa’, kuma duk cikin fina-finan da na yi babu wanda ya fito da ni aka sanni sai fim ɗin ‘Fanan’, don haka ne ma wasu sai a yanzu su ka fara sani na duk da cewar na daɗe, kuma akwai wasu fina-finan da na fito a matsayin jaruma, amma dai ina ganin yanzu ne lokacin na wa ya zo.

To, ya aka yi kika samu shiga fim ɗin ‘Fanan’?
Na samu kaina a cikin fim ɗin ‘Fanan’ ne ta dalilin furodusar fim ɗin Mansurah Isah, wadda ita ce ta kira ni ta faɗa mini cewar tana son na fito a rol ɗin Fanan a fim ɗin saboda na yi daidai da rol ɗin, don haka ina godiya a gareta, babu abin da zan ce da ita sai dai Allah ya saka mata da alheri.

Rawar da kika taka a fim ɗin ya sa fuskarki ta fito kowa ya sanki. Ko ya kike ganin tasirin fim ɗin a rayuwar ki?
To gaskiya na ji daɗi sosai fiye da yadda kake tunani, don ban taɓa tunanin zan samu ɗaukaka a cikin ɗan lokaci kaɗan ba, don haka ko lokacin da a ke nuna shi a sinima idan na ga yadda mutane suke son su ganni ina jin daɗi sosai, har na ke ji a zuciyata wai ni ce a ke zuwa a na kallo na har a da yin hotuna da ni saboda na zama jaruma, don haka har hawaye ne yake zuba daga idona, don haka gaskiya fim ɗin ya yi mini tasiri sosai, ina alfahari da shi. Don fim ɗin ya ɗaukaka ni a daidai lokacin da ban zata ba.

Ko a wajen ɗaukar fim ɗin kin sha wahala sosai ganin cewar fim ɗin cike yake da abin tausayi?
Eh to, gaskiya zan iya cewa na sha wahala, kuma a wani wajen ban sha wahala ba, kuma ko da na sha wahala a wajen aikin, to sakamakon da na samu na nasara daga baya ya sa ba na ganin wahalar, don haka ma na manta da wahalar da na sha.

To, cikin aikin me ya fi burge ki?
Gaskiya abin da ya fi burge ni shi ne, yadda na yi aiki da daraktan ba tare da ya nuna mini wani abu na takura ba, har mu ka gama ina cikin jin daɗi, don ko da wani abu na yi ba daidai ba, to zai nuna mini cikin sauƙi yadda zan fahimta. Don haka mun yi aikin fim ɗin cikin sauƙi da kwanciyar hankali.

Sabira tare da Sani Danja

A farkon fim ɗin an nuno ki a matsayin matar da mijinta yake azabtar da ita. Ko ya kika kalli kanki a wannan matsayin?
To gaskiya ni kaina sai da na ji tausayin kaina, saboda ban taɓa yin rol irin wannan ba, don haka sai abin ya ba ni tausayi, kuma na yi mamaki ma da har na iya gudanar da aikin.

Sai kuma mu ka ga a ƙarshen fim ɗin kin zama matar babban mai kuɗi ko?
Eh, gaskiya ne hakan ya nuna cewar wahala ba ta ɗorewa, kuma daɗi ma haka, don irin saƙon da fim ɗin ya ƙunsa kenan.

Wanne irin buri kika sa a gaba?
To, burina dai na ƙara yin nasara a gaba, don haka kullum addu’a na ke yi, Allah ya qara ɗaukaka ni, kuma ina fatan komai zai zo mini cikin sauƙi. Kuma Ina fatan masoyana za su taya ni da addu’ar Allah ya qara ɗaukaka ni a cikin harkar fim ɗin.

To madalla, mun gode.
Ni ma na gode sosai.