Fim ɗin Gari Guda zai buɗe sabon shafin kallo a sinima – Darakta Sufyanu Kabo

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

A yanzu dai duk wani shiri ya kammala na fitowar sabon fim ɗin ‘Gari Guda’, wanda Kamfanin ‘Islamic Film Empire’ suka shirya, kuma Sufyanu Lawal Kabo ya bayar da Umarni.
Ganin yadda fim ɗin ya bambanta da sauran fina-finan da aka saba shirya wa a masana’antar fina-finai ta kannywwod ne ya sa muka nemi jin ta bakin Daraktan fim ɗin Sufyanu Lawal Kabo don jin irin abubuwan da fim ɗin ya ƙunsa. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance:

Akwai wani sabon fim da ka yi aikin sa, kuma ka ke shirin gabatar da shi ga jama’a a wannan lokacin, don haka mu ke so ka yi wa masu karatun mu bayani kan manufar shirya fim ɗin da kuma abubuwan da ya ƙunsa. 
To shi wannan fim sunan sa ‘Gari Guda’, kuma mun samar da shi ne a ƙarƙashin kamfanin shirya Fina-finai na ‘Islamic Films Empire’, kuma daman mun kafa wannan kamfanin ne domin mu samar da fina-finai waɗanda su ka shafi koyar da tarbiyyar Muslunci da kuma koyar da kyakyawan ɗabi’u a cikin tsari na fina-finan mu na Hausa, wannan shi ne manufar mu ta samar da shi wannan kamfanin ma. 

Kuma shi wannan fim mai suna ‘Gari Guda’ kamar yadda ka faɗa muna shirin gabatar da shi ga jama’a, domin za mu fara haska shi a wasu daga cikin sinimu na ƙasar nan, musamman ma dai a nan Kano da sauran manyan birane.  Kuma gaskiya shi wannan fim ɗin, ba kamar sauran fim ba ne da mutane su ka saba gani, duk da cewa mutanen da su ke kallon fim a yanzu, kashi biyar ne cikin ɗari su ke zuwa Sinima kallon fim, to kuma kusan a yanzu kallon fim ɗin ya koma Sinima. 

To bayan Sinimar a yanzu muna ta bin wasu hanyoyi na wayar da kan jama’a domin su waye da kallon fim a Sinima su daina kyamatar ta. Kuma su gane wannan fim ɗin ba kamar waɗanda su ka saba kallo ba ne a baya wanda ya sa su ke gudun kallon finafinan. Don haka za mu jawo hankalin mutane ma su hankalin don su zo da yaran su da matan su, su kalla, wannan shi ne tunanin mu a game da wannan fim ɗin na ‘Gari Guda’.

Da ya ke ka faɗi cewar kun kammala shirin ku na shirin fara haska wannan fim ɗin, ko kun fitar da rana? 
To in Allah ya yarda kamar yadda muka tsara kuma mu ke sa ran hakan ta kasance, mu na son mu fara nuna fim ɗin daga ranar 19 ga wannan watan na Nuwamba, wanda zai kasance an haska shi a Sinimar da ke cikin ‘Shoprite’. Sai kuma Sinimar Platinum da ke titin Zaria duk a Kano, sannan kuma daga baya za mu yi tsarin da za a fara haskawa a Legas da sauran manyan biranen ƙasar nan, har ma da ƙasashen waje in Allah ya yarda. 

To ko bayan sinima ko akwai wani waje da ku ke sa ran za ku kai shi ku haska don saƙon ya isa cikin sauƙi ga mutane waɗanda ba sa zuwa Sinima? 
To kamar dai yadda mutane su ka saba, daga Sinima babu wajen da a ke kai fim, sai dai a saka shi a ‘YouTube’, kuma gaskiya mu wannan fim ɗin da mu ka yi ba fim ne na ‘YouTube’ ba, saboda haka idan ma za mu saka shi a ‘YouTube’ ɗin to ba abu ne na kwana kusa ba. Don haka duk wanda ya ke buqatar ya kalli fim ɗin, abin da zai fi masa sauƙi ya tafi Sinima ya kalla a lokacin da a ke haskawa. Domin babu wata rana da mu ke tunanin za mu saka shi a ‘YouTube’, sai dai idan hali ya bayar na a yi hakan. Sai dai akwai shirin da mu ka yi na haskawa a manyan gidajen Talbijin zuwa nan gaba. 

Daga ƙarshe wanne kira za ka yi ga jama’a? 
To kira na dai shi ne mutane su san irin fim ɗin da za su kalla, don yanzu duniya ta yi nisa da ilimi, saboda haka ne ma muka shirya fim ɗin ‘Gari Guda’ don ya zama salon fim ɗin ma da a ke yi na Hausa ya zama ya canza, ta yadda za a rinka saka kyawawan ɗabi’un mu da kuma addinin mu, don haka ina kira ga mutane da cewar, lokaci ya yi da za su rinƙa tantance fim ɗin da za su kalla masu ma’ana ba masu nuna sharholiya ba. 

Madalla, mun gode. 
Ni ma nagode sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *