Fursunoni huɗu sun samu shaidar digiri bayan kammala karatu a NOUN

Daga BASHIR ISAH

Wasu fursunoni huɗu daga gidan gyaran hali da ke yankin Kuje a birnin tarayya Abuja, kowannensu ya samu shaidar digiri bayan kammala karatu a Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN).

Kwanturola mai kula da gidan gyaran hali na Abuja, Abdul-rahman Maiyaki ne ya bayyana hakan yayin bikin yaye ɗaliban wanda ya gudana a Talatar da ta gabata a Abuja. Tare da cewa cibiyoyin gyaran hali wurare ne da ake gayara ɗabi’un fursunoni don kyautata musu rayuwa.

Maiyaki ya ƙara da cewa cibiyar wuri ne da ake gyara halayen fursunoni domin su koma su zama nagartattu a cikin al’umma.

Daga nan, ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga sauran fursunonin da ke karatu da su ɗauki lamarin karatunsu da muhimmanci.

Haka nan, ya yi kira ga sauran fursunonin da su yi ƙoƙari su ci moriyar wannan dama da NOUN ta ba su wajen yin karatu don samun shaidar digiri.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya rawaito Maiyaki na cewa, “Wannan shiri na bai wa fursunoni damar karatu na taka muhimmiyar rawa wajen ganin rayuwar fursunonin ta kyautata ta yadda al’umma za ta amfana da su bayan sun fita.”