Google ya haramta tallata bayanan siyasa a shafukansa a Philippine

Daga BASHIR ISAH

Kamfanin Google ya bayyana cewa, ba zai lamunci tallata bayanan siyasa ba a shafukansa.

Rashin amincewar kamfanin na da nasaba da babban zaɓen ƙasar Philippine da za a gudanar shekara mai zuwa.

Da yake ƙarin haske game da yaɗa bayanan siyasa a shafukansa kamfanin Google ya ce, “Dangane da zaɓaɓɓukan Philippine na 2022, ba a yarda a yaɗa bayanan siyasar ƙasar ba kama daga ranar 8 ga Fabrairu zuwa 9 Mayu, 2022.

“Tallar siyasa talla ce da ke tallata jam’iyya ko ɗan takara ko akasin haka don neman jagorancin al’umma.”

Ma’aikatar Zaɓe ta Philippine ta ce, 8 ga Fabrairun 2022 ita ce ranar da aka tsayar a hukumance don soma gudanar da yaƙin neman zaɓe a ga masu neman muƙamai a matakin ƙasa, yayin da masu neman muƙamai ƙasa da haka za su soma nasu yaƙin neman zaɓen ya zuwa 25 ga Maris.

Ma’aikatar ta ce, “Google ba zai yarda da tallace-tallacen zaɓe ba a shafukansa a faɗin ƙasar Philippine, sai dai kamfanin zai maida hankalinsa wajen yin abin da zai taimaka wajen wayarwa da kuma ilimantar da ‘yan ƙasar game da harkokin zaɓen.

Ko a baya, Google ya ɗauki makamancin wannan mataki inda ya haramta tallata bayanan siyasa a shafukansa yayin zaɓen Canada a 2019 da kuma Singapore a 2020.