Gwamna Zulum ya sake lashe zaɓen gwamna a Jihar Borno

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Maiduguri

Sakamakon da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta sanar na zaɓen Gwamna da ya gudana a jihar Borno a ranar Asabar, ya bayyana Babagana Umara Zulum na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamna da ya gudana a jihar.

Da yake bayyana sakamakon da yammacin Litinin, Baturen zaɓen, Jude Rabo, ya ce ɗan takarar jam’iyyar APC, Babagana Zulum, shi ne ya lashe zaɓen da ƙuri’u 545,542.

Yayin da babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Mohammed Jajari ya samu ƙuri’u 82,147.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *