Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin yaƙi da yunwa a Keffi

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya, a ƙarƙashin Ma’aikatar Agaji, Jinƙai da Kyautata Rayuwar ‘Yan Ƙasa, ta ƙaddamar da shiri na musamman kan yaƙi da yunwa mai taken ‘Project Zero Hunger’ a ƙaramar hukumar Keffi, jihar Nasarawa.

Taron ƙaddamarwar ya gudana ne a ƙofar fadar masarautar Keffi a ranar Alhamis, tare da raba kayayyakin masarufi ga mutum sama da ɗari, maza da mata.

Kayayyakin da aka raba sun haɗa da;
shinkafa, wake man girki, magi, tocila, omo, atampa, sabulai da sauransu, wanda aka kimtsa su cikin wani akwatin roba na musamman.

Da yake jawabi a madadin Hon. Kwamishina Iman Sulaiman Ibrahim wadda ita ce jagorar ƙaddamar da shirin, Bello Muhammad Bello wanda darakta ne a ma’aikatar, ya bayyana cewa an samar da wannan shiri ne musamman don tallafa wa nakasassu da marasa galihu da kayan masarufi don kyautata rayuwarsu.

Sama da mutum ɗari ne suka ci gajiyar wannan shiri wadanda aka tsinto su daga sassan yanki, kuma ake sa ran tallafin zai taimaka wajen rage musu raɗaɗin rayuwa.

Da yake sanya wa shirin albarka, Mai Martaba Sarkin Keffi, Dr. Shehu Chindo Yamusa III, ya yaba wa Gwamnatin Tarayya da wannan namijin ƙoƙari, tare da nuna godiyarsa kasancewar an zaɓi garin Keffi a matsayin inda aka soma ƙaddamar da shirin.

Binciken MANHAJA ya gano cewa baya ga Ƙeffi, haka ma an ƙaddamar da shirin a Abuja da kuma yankin Karu, kuma haka ake sa ran ci gaba da ƙaddamar da shirin a sassa har a kewaye ƙasa baki ɗaya.

Taron ya samu halarcin jami’an gwamnati na tarayya, jiha da ma ƙaramar hukumar Keffi, ciki har da ɗan Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa mai wakiltar Keffi ta Gabas, Hon. Abdulazeez SK Danladi wanda shi ne mai mausakin baki kuma jagoran raba kayayyakin, sai kuma takwaransa mai wakiltar Keffi ta Yamma, Hon Baba Ali Nana da sauransu.

Baki ɗayan waɗanda suka amfana da shirin, sun yi matuƙar farin ciki tare da fatan alheri ga gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *