Hajjin 2021: NDLEA ta buƙaci a hori maniyyata su guji mu’amala da miyagun ƙwayoyi

Daga AISHA ASAS

Hukumar Yaƙi da Fatauci da Tu’ammali da Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), ta yi kira ga Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) da ta wayar da kan maniyyata da ke shirin tafiya ƙasa mai tsarki da su guji yin mu’amala da muggan ƙwayoyi yayin aikin Hajjin 2021.

Kwamandan NDLEA na jihar Neja, Haruna Kwetishe ne ya yi wannan kira yayin ziyarar da ya kai wa hukumar kula da walwalar maniyyata ta jihar da ke Minna, babban birnin jihar.

Haka nan, Kwamandan ya yi kira ga jami’an gwamnati da su tabbatar da cewa waɗanda aka amince wa zuwa ƙasa mai tsarki ɗin mutane ne masu kamun kai. Tare da bada tabbacin jami’an NDLEA za su kasance a dukkanin sansanonin alhazai da ake da su a faɗin ƙasa domin tantance miyagu daga maniyyatan.

Alhaji Umar Makun Lapai, wanda shi ne sakataren hukumar alhazai na jihar, baya ga yabo da ya yi da ziyarar NDLEA ya kuma ce hukumar ba ta taɓa samun wani maniyyaci a jihar da yin mu’amala da safarar miyagun ƙwayoyi zuwa ƙasa mai tsarki ba.

Sakataren ya ci gaba da cewa hukumarsu a shirye take ta yi aiki tare da NDLEA wajen duba maniyyata. Ya ce tuni hukumarsu ta bai wa jami’anta horo a fannoni daban-daban haɗa da abin da ya shafi yaƙi da miyagun ƙwayoyi duk dai da manufar samun natsattsen aikin Hajji a 2021.