HOTUNA: Yadda aka gudanar da jana’izar hamshaƙin ɗan kasuwa, Sani Dahiru Yakasai

A ranar Juma’a aka gudanar da jana’izar hamshaƙin ɗan kasuwar nan, Sani Dahiri Yakasai.

An gudanar da sallar jana’izar ce a Fadar Sarkin Kano.

Ranar Alhamis Allah Ya yi wa marigayin cikawa a ofishinsa bayan fama da rashin lafiya.

Mahalarta jana’izar sun haɗa da Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, Sanata Ibrahim Shekarau, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran ɗaruruwan Musulmi.