Hukumar SON ta bada shaidar ingancin kaya ga kamfanoni 13 a Kano

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar nan mai tabbatar da ingancin kayayyaki ta Nijeriya ta miƙa takardun shaidar tantancewa da tabbatar da inganci (MANCAP) ga wasu kamfanoni 13 a Kano. Hakan ta faru ne ranar alhamis 23 ga Oktoba, 2021.

A jawabinsa, Darakta Janar na hukumar SON, Malam Faruk Salim, wanda shugaban tsare-share na yanki, Mista Usman Muhammad ya wakilta, ya bayyana cewa, wannan shaidar tantancewar da tabbatar da ingancin kaya, (MANCAP) dole ce ga dukkan wani mai riƙe da ƙananan masana’antu ko kamfanoni. 

Ya ƙara da cewa, ita takardar shaidar ta MANCAP ita ce shaidar da za ta tabbatar da cewa, ƙananan kamfanoni da masana’antu su ma sun cika sharuɗɗan da ake buƙata ga dukkan kamfanonin Nijeriya su cika shi domin tabbatar da tsaro da kuma lafiyar al’ummar da za su saya su yi amfani da kayan.

A cewar sa, su waɗannan kamfanoni 13 da aka zaɓa aka ba wa shaidar, su ma sai da suka bi matakan bincike da tacewa, har sai da aka tabbatar da inganci da cancantar a yi amfani da kayansu.

Hakazalika, Darakta Janar ɗin ya shawarci kamfanonin a kan su tabbatar da cewa, lambar shaidar da suka amsa, sun yi amfani da ita kaɗai ne a kan iyakacin kayan da aka tantance kawai ne. Wato waɗanda suka haye waccan tantancewar da aka yi. 

Sannan ya yi jan kunne ga kamfanonin a kan karya dokar yarjejeniya inda ya ce yin hakan zai iya jawo a ɗauki matakin dakatar da shaidar kamfani ko ma a ƙwace ta gabaɗaya. 

Ita dai wannan shaida ta MANCAP shaida ce da aka ƙirƙire ta tun a shekarar 2006 domin tabbatar da an samar da ingantattaun kayayyakinsu sun samu inganci kamar na manyan kamfanoni a cewar shugaban tsare-tsare na SON, Malam Yunusa Muhammad.