Ina mafita a musayar kalamai tsakanin Gwamnatin Kaduna da Ƙungiyar Ƙwadago?

Daga AMINU ƊANKADUNA AMANAWA, Sokoto

Wani babban abin da ya fi jan hankalin jama’ar Nijeriya a wannan lokacin da ake ciki, bai wuce turka-turkar da ke wakana ba tsakanin Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i, da Ƙungiyar Ƙwadago (NLC), wacce shugabanta na ƙasa, Kwamred Ayuba Wabba, ke jagorantar gudanar da zanga-zangar ƙin jinin matakin da gwamnan na Kaduna ya ɗauka na dakatar da ma’aikatan ƙananan hukumomi da wasu tarin ma’aikatan jihar da sunan rage yawan kuɗaɗen da ma’aikatan ke laƙumewa na ɗan abin da jihar ke samu daga Gwamnatin Tarayya.

Wannan kusan shine abinda bayanai, kafofin yaɗa labarai dama waɗanda lamarin ya shafa ke bayyanawa a matsayin dalilin da shi gwamnan ke bayyanawa da ya sanya ɗaukar matakin dakatar da ma’aikatan a lokacin da dubban ɗalibai a jihar suka kammala karatu a manyan makarantun gaba da sakandare daban-daban da ke ciki da wajen jihar ta Kaduna da ke da burin samun aikin dogaro da kansu, domin tallafa wa kansu da iyalansu.

Baya ga wannan ma, jihar ta Kaduna kusan na daga cikin jihohin da matsalar tsaro ke addaba kama da ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, rikicin ƙabilanci da na addini da sauransu, da galibi masu lura kan lamuran yau da kullum ke alakantawa da rashin ayukkan yi da jama’a ke fama da shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke zama tarnaƙi da ɗorewar zaman lafiyar, duk wata gwamnati da ta ƙasa shawo kan matsalar rashin ayyukan yi musamman ga matasa, koma koyar da su sana’o’in hannu, kamar yadda da yawa daga cikin masu lura kan lamuran na yau da kullum ke bayyana.


Koda yake ba wannan ne karon farko ba da gwamnan ke ɗaukar irin matakin da ake ganin ya saɓa doka na korar ma’aikata, inda ko a baya sai bayanai suka ambato gwamnan ya dakatar da malaman makarantun jihar da sunan samar da ingatattun da za su ciyar da ilimin jihar ta Kaduna a gaba, ganin yadda ɓangaren ke da nakasu na iya cimma nasarar da aka tsara 100 bisa 100 na samar da ingataccen ilimi ga yaran jihar ta Kaduna.

Duk da yake a wani ɓangare za a iya duba cikin tsanaki kan dalillan da suka sanya gwamnan ɗaukar wannan matakin, amma a irin wannan hali da yanayin da ake ciki ɗaukar irin wannan matakin sam bai kamata ba, domin galibin ma’aikatan aikin da suke gudanarwa kusan shine abinda suka dogara wajen ciyar da iyalansu, da ma tallafa wa abokan arziki su iya tafiyar da rayuwar cikin rufin asiri.

“Duk dan daya hana babarsa bacci, to fa tabbas shi ma fa ba zai runtsa ba. Wannan kusan karin magana ne da Malam Bahaushe kan yi amfani da shi wajen fitar da saƙon da ke zuciyarsa a fakaice, koda arashi da masu iya magana kance ya kamma baƙauye, domin kuwa sanin ko wane Gwamnan Jihar ta Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i na daga cikin sahun gaba-gaba da a baya yasha shiga a sahun ‘yan ƙwadago, domin gudanar da zanga-zanga kan lamurran da suka shafi kasa, musamman na tsaro a lokacin gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan.

Sai dai wanzam ba ya son jarfa. Abin da ya fi ba wa mutane mamaki da shine irin kalaman gwamnan a kwana na biyu da aka shiga zanga-zangar, na neman Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), Kwamred Ayuba Wabba, bisa zargin sa da yunƙurin durƙusar da tattalin arzikin jihar a zanga-zangar da suke, wacce ta kai da dakatar da harkokin yau da kullum na aiki, kasuwanci, sufuri da ma hasken wutar lantarki, baya ga wannan ma, a wata sanarwa da ta ce, “gwamnati za ta kori dukkanin ma’aikatan jinya da ba su kai matakin aiki na 14 ba saboda yajin aikin da suka shiga ba bisa ƙa’ida ba, da yi ma na barazanar korar duk wani ma’aikacin jami’ar jihar  da ya ƙaurace wa aiki.

“Da ma ga umarnin da gwamnati ta bayar ga dukkanin ma’aikatun jihar nasu gabatar da rijistar ma’aikatan da ke zuwa aiki ga sakataren gwamnati da kuma kwamishinan ilimi.”

Lamarin dai kusan ya so ya koma almara ko wasan kalamai tsakanin gwamnatin da kungiyar kwadago, inda a bayanin Kakakin NLC na ƙasa, Kwamred Nasir Kabir, ya bayyana cewa, ita ƙungiyar na