INEC ta tsayar da ranar bayyana sakamakon zaɓen Gwamnan Adamawa

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta tsayar da ranar da za ta bayyana sakamakon zaɓen Gwamnan Jihar Adamawa.

Ya zuwa ranar Alhamis ake sa ran INEC ta bayya sakamakon zaɓen na Adamawa.

A cewar Kwamishina a hukumar, Dr Festus Okoye, INEC za ta yi zama a ranakun Talata da Laraba don tattauna batun.

A ranar Litinin INEC ta dakatar da Kwamishinan Zaɓe na Jihar Adamawa (REC), Hudu Yunusa Ari, saboda riga-malam-masallacin da ya yi wajen karɓe ikon Baturen Zaɓe tare da bayyana ‘yar takarar Jam’iyyar APC, Sanata Aisha Dahiru Binani, a matsayin wadda ta lashe zaɓe tun kafin kammala tattara sakamakon zaɓen lamarin da ya haifar da cece-kuce daga ɓangarori daban-daban.

INEC ta gayyaci Ari da Baturen Zaɓen, Mele Lamido, zuwa Babban Ofishinta a Abuja don jin ba’asi.

Bayanai sun ce sa’ilin da Ari ya bayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓe, sakamakon ƙananan hukumomi 10 aka samu haɗawa yayin da ake zaman jiran na ragowar.

Lamarin da ya sa ɗan takarar jam’iyyar PDP kuma Gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri da ita kanta jam’iyyar suka nuna rashin yardarsu kan bayyana nasarar Binani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *