INEC ta tsayar da ranar gudanar da zaɓen Adamawa da sauransu

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta tsayar da ranar da za ta gudanar da zaɓen gwamnan da na majalisar tarayya da na jihohi a wuraren da zaɓe bai kammala ba.

INEC ta ce ya zuwa ranar 15 ga Afrilun 2023 za ta gudanar da zaɓe a wuraren da lamarin ya shafa.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta shafinta na Tiwita a ranar Litinin.

“Bayan taro da aka yi yau, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta yanke gudanar da dukkan zaɓukan gwamna, na ‘yan majalisar tarayya da na jihohi da suka yi saura a ranar Asabar, 15 ga Afrilun 2023.

“Ƙarin bayani na nan tafe ba da jimawa ba,” in ji sanarwar.