Kakakin Majalisar Dokokin Zamfara da mataimakinsa sun dafa ƙasa a zaɓen ranar Asabar

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Zamfara kums ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Zurmi ta Gabas, Hon. Nasiru Mu’azu Magarya, ya sha kaye zaɓen gwamna da na majalisar jiha da aka gudanar ranar Asabar ɗin da ta gabata.

Haka mataimakinsa, Hon. Musa Bawa na Jam’iyyar APC, mai wakiltar mazaɓar Tsafe ta Yamma, bai kai bantensa ba a zaɓen

Baturen zaɓen, Mudasiru Samaila, ya ce, Mu’azu ya samu ƙuri’u 13,820 ne a zaɓen, yayin da abokin hamayyarsa na Jam’iyyar PDP, Bello Muhammed ya samu ƙuri’u 21,197.

“Don haka ɗan takara Jam’iyyar PDP ne ya samu nasara kujerar Majalisar dokoki mai wakiltar Zurmi ta Gabas,” in ji jami’in.

Wannan na nuni da cewa Kakakin Majalisar ya rasa damarsa ta sake komawa kujerarsa.

Ɗan takara Bilyaminu Samaila na jam’iyyar PDP, shi ne ya doke Mataimakin Kakakin da ƙuri’u 11,213.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *