Kannywood: An gudanar da taro kan haƙƙin mallaka a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano

Ƙungiyar kare haƙƙin mallaka na hoto mai motsi wato (Audio Visual Rights Society of Nigeria -AVRS) ta gudanar da taro na musamman, da dukkanin masu ruwa da tsaki, waɗanda ke amfani da kayan kirkira na hoto mai motsi, a Jihar Kano.

Taron, wanda da ya gudana a Kannywood Hall da ke kan titin Muhammadu Buhari, a Tudun-Yola da ke cikin birnin Kano.

Tunda farko a jawabinsa shugaban ƙungiyar na ƙasa Mahmood Ali-Balogun, ya ce, maƙasudin taron shi ne, karɓo haƙƙoƙin finafinan da ake haskawa a otel-otel da wuraren cin abinci da wuraren aski da manyan Bas bas da sauransu.

Ya qara da cewa, “an kafa ƙungiyar shekara shida zuwa bakwai da suka wuce, aikin ƙungiyar shi ne, ta karɓo haƙƙoƙi, kuma ta rabawa membobinta wanda mafi yawansu ‘yan fim ɗin ba za su iya karɓowa ba.”

Kuma ya ce, dole ne sai ka yi rigistar sannan ne za ka ci gajiyar wannan ƙungiyar wanda bai yi rigistar ba ba zai ci gajiyar wannan ƙungiya ta AVRS ba.

Ɗaya daga cikin daraktocin ƙungiyar wanda kuma jigo ne a masana’atar ta Kannywood Sani Muazu, ya ce, “yana da matuqar muhimmanci duk mai harkar fim ace yana ciki ba don komai ba sai don gajiyar da mai harkar fim zai ci da wannan ƙungiya.”

Ya ƙara da cewa, “da yawan mu mun yi aiki shekara da shekaru, amma ba ma samun gajiyar waɗannan ayyuka, kuma muna ganin mutane suna amfani da ayyukanmu a wurare na kasuwanci, to gwamnati a iya tunaninta ta ga ya dace a ce ta kafa wata hukuma ta AVRS wacce za ta karɓo mana wannan gajiyar daga cikin waɗanda suke amfani da ayyukanmu wuraren da ba ma nan.

Ni na shiga cikin wannan ƙungiyoyi kuma na ci amfaninta, Ina kan ci, domin yanzu shekara 2 kenan ana aiko min da kuɗi, Ina zaune sai inga alert an turo min kuɗi saboda gajiyar aikin da na yi a baya.”

Taron ya samu halartar manyan baƙi da suka haɗa da: Shugaban MOPPAN na ƙasa Dr. Ahmad Sarari da na Jihar Kano Malam Ado Ahmad Gidandabino MON da mataimaki na musamman ga Gwamnan Kano akan Kannywood Malam Khalid Musa da Editan Blueprint/Manhaja Malam Nasir S.

Gwangwazo da shugaban masu otal-otel na Jihar Kano da shugaban ‘yan Downloading na Kano da shugaban ‘yan wasa Alasan Kwalli da Shaubu Lilisko da Hajiya Balaraba Ramat Yakubu da Kamal S. Alkali da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *