Kwastam ta kama kwantena maƙare da miyagun ƙwayoyi a Legas

Daga WAKILINMU

Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Ƙasa da ke yankin Apapa a jihar Legas, ta ce ta kama wani sunduƙin safarar kayayyaki maƙare da ƙwayoyin taramol da kodin waɗanda masu tu’ammali da miyagun ƙwayoyi kan yi amfani da su don shiga yanayi na maye.

Bayanan hukumar sun nuna a Litinin da ta gabata jam’ian hukumar suka kama sunduƙin a Legas mai ɗauke da katan-katan na ƙwayar taramol guda 124 da na kodin guda 805.

Rahotanni sun ce masu fasa-ƙwaurin sun yi ɓad da sawu ta hanyar ɗora tukwane a kan ƙwayoyin da nufin kada jami’an kwastam su gano shirinsu.

A kwanan ne Shugaban Shiyya na hukumar da ke Apapa, Malanta Yusuf, ya baje kwatankwacin kayayyakin da suka kama na ƙwayoyin da aka yi safararsu.

Shugaban ya bai wa al’umma tabbacin cewa hukumar za ta ci gaba da matse ƙaimi wajen yaƙi da harkokin fasa-ƙwauri musamman ma abin da ya shafi miyagun ƙwayoyi.