Lai ga ‘yan Nijeriya: Ƙasa na cikin aminci, babu buƙatar tada hankula

Daga WAKILINMU

Minista Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa duk da matsalolin tsaron da ƙasa ke fuskanta, Nijeriya na cikin aminci ƙarƙashin gwamnatin Buhari.

Da wannan ministan ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da kada su ji ɗar game da yanayi mara kyau da hasashen masu hasashe ke dangana ƙasar da shi.

Lai ya faɗi haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Oluyin na Iyin-Ekiti, Sarki Adeola Adeniyi Ajakaiye da tawagarsa a Alhamis a ofishinsa da ke Abuja.

A cewarsa, “Duk da ƙalubalan tsaron da ake fuskanta, ina so in yi amfani da wannan dama wajen tabbatar wa ɗaukacin ‘yan Nijeriya cewa ƙasa na cikin aminci a hannun amintattu. Kada mu yarda da hasashe mara daɗi da ake yi ya wa ƙasa.

Ministan ya ce abu ne mai matukar muhimmanci shugabanni a dukkanin matakai da su riƙa bai wa jama’a saƙonni masu ƙarfafa gwiwa a maimakon faɗin kalaman da za su haifar da tsoro a cikin zukatan al’umma.