Masu sulhu a Sudan na ƙoƙarin mayar da hamɓararriyar gwamnati

Masu shiga Tsakani a Sudan sun fara tattaunawa a wani yunƙuri na dawo da hamɓararriyar gwamnatin firaminista Abdallah Hamdok da Sojoji suka yi wa juyin mulki a makon jiya bayan kiraye-kirayen ƙasashe ciki har da Amurka da Majalisar Ɗinkin Duniya.

Tun farko ƙasashen Amurka da kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ne suka buƙaci Sudan ta dawo da gwamnatin da aka hamɓarar yayin juyin mulkin na makon jiya da ke biyo bayan boren da ‘yan ƙasar suka shafe makwanni suna yi bisa buƙatar ganin Firaminista Abdallah Hamdok ya sauka daga mulki.

Tuni dai ɓangarorin fararen hula da na gwamnati suka fara tattaunawa a birnin Khartoum, ganawar da ta ƙunshi jagoran juyin mulkin Abdel Fattah al-Burhan da tsohon jagoran ‘yan tawayen ƙasar baya ga hamɓararren Firaministan ƙasar Abdallah Hamdok.

Kakakin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke cikin ma su shiga tsakani a rikicin na Sudan ya ce ana samun gagarumar ci gaba a tattaunawar wadda ake fatan ta lalubo rarrabuwar kan da ɓangarorin biyu ke da shi don magancewa.

Tsohon shugaban hafson sojojin Sudan Imad Adawi, yayin zantawarsa da manema labarai a birnin Alƙahira na Masar, ya ce, akwai yiwuwar cimma jituwa tsakanin ɓangarorin biyu cikin sauri.

Masu shiga tsakanin da ke cikin tattaunawar akwai fitattun mutane daga cikin Sudan sai wakilan Sudan ta kudu da na Majalisar Ɗinkin Duniya baya ga wasu daga sauran ƙasashen Afrika.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *