Matawalle ya sake naɗa wasu daga cikin mashawartansa da ya kora

Daga Sanusi Muhammad, a Gusau

A Litinin da ta gabata, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya sake naɗa mutum takawas daga cikin masu ba shi shawara na musamma da ya sauke kwanan nan.

Bayanin sake naɗa masu bai wa gwanan shawara na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun Babban Sakataren Harkokin Majalisar Gwamnan, Yakubu Haidara, a madadin sakataren riƙo na gwamnatin jihar, Alhaji Kabiru Balarabe

Waɗanda naɗin ya shafa su ne; Aminu Abdullahi-Alkali, Ahmed Muktar-Mohammed, Junaidu Aminu-Kaura, Ibrahim Ma’aji-Gusau, Dr Aslam Aliyu, Yusuf Abubakar-Zugu, Danyaro Abdullahi-Wuya, da kuma Abubakar Musa (Mainera).

Sanarwar ta nuna naɗin nasu ya soma aiki ne nan take.

Idan dai za a tuna, a ranar 3 ga Yuli ne Gwamna Matawalle ya bayyana soke duka masu ba shi shawara na musamman ba tare da ya sanar da dalilin ɗaukar matakin hakan ba.