Matawalle ya ziyarci waɗanda rikicin ‘yan bindiga ya shafa a Anka, Bukkuyum

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed (Matawallen Maradun) ya ziyarci ƙananan hukumomin Anka da Bukkuyum a ranar Asabar da ta gabata domin jajantawa tare da tantance irin ɓarnar da aka yi wa waɗanda harin ‘yan bindiga ya rutsa da su a yankunan.

Gwamna Matawalle ya yi Allah wadai da yadda kafafen yaɗa labarai suka riƙa yaɗa rahotannin da babu gaskiya na mace-macen da ke faruwa a hare-haren ‘yan bindiga na baya-bayan nan.

Yayin da yake a fadar Sarkin Anka da Bukkuyum, Gwamna Matawalle ya jajanta wa sarakunan biyu da ɗaukacin al’ummarsu kan wannan mummunan lamari da ya faru tare da yin alƙawarin magance matsalar jin ƙai da ke tasowa sakamakon hare-haren.

Gwamnan ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai na yanar gizo da na soshiyal midiya da su riƙa tantance gaskiyar lamarin maimakon tsoratar da jama’a kan kowane dalili.

A cewarsa, “a fili yake cewa ba ‘yan fashi a daji ne kawai ke yi wa gwamnatinmu barazana ba, har da wasu tsirarun ‘yan siyasa a garuruwa da kauyukanmu.”

Daga nan ya zargi wasu ‘yan siyasa da rura rikicin don neman wata manufa ta siyasa da kuma masu ba da labari da ke taimaka wa ‘yan fashin wajen aikata munanan ayyukansu.

Ya ce, “Duk za mu ci nasara da ikon Allah.”

Daga nan sai ya sanar da cewa daga yanzu gwamnati za ta ɗauki waɗanda suka bayar da rahoton ƙarya da gangar na ‘yan bindigar da suka tsere a matsayin ‘yan ta’adda.

“Ba za mu iya naɗe hannayenmu ba mu ƙyale mutane su haifar da firgici a koyaushe, kuma su zana hoto na ainihin abubuwan da ke faruwa a jihar da muka fuskanci babban gwaji wanda muke yin iya ƙoƙarinmu don magancewa,” inji Matawalle.

Gwamnan ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa za ta haɗa kai da Gwamnatin Tarayya a ƙoƙarinta na ganin an kawo ƙarshen ‘yan fashi a jihar.

Haka nan, ya yaba wa Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari bisa jajircewar da ta yi wajen magance matsalar rashin tsaro a ƙasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *