Matsalar tsaro: Hannu da yawa maganin ƙazamar miya

Ba da jimawa ba ne ofishin jakadancin ƙasar Amurka a Nijeriya ya fitar da wata sanarwa da ke shawartar ‘yan ƙasar da ke nan Nijeriya da ma masu niyyar shigowa, su dakata ko kuma su yi hattara, sakamakon wasu rahotannin sirri da aka ce an samu na yiwuwar kai hari wasu muhimman wurare a ƙasar nan, musamman ma dai Babban Birnin Tarayya Abuja.

A wasu rahotannin ma an ce ofishin jakadancin ƙasar Birtaniya a Nijeriya shi ma ya sake tabbatar da wannan rahoton.

A yayin da hukumomin tsaro a Nijeriya ke ƙoƙarin gudanar da nasu binciken don tabbatar da ingancin wannan rahoto, an buƙaci ‘yan ƙasa su ƙara lura da kiyayewa, a duk inda suke, domin kaucewa faɗa wa cikin fitinar da ake fargabar faruwarta.

An ce dai ruwa ba ya tsami banza, don haka tilas ‘yan Nijeriya su tashi tsaye, ba ga gwamnati, ko jami’an tsaro kaɗai ba, kowa na da gudunmawar da zai bayar don ganin masu wannan mugun nufi ba su cimma burin su ba.

A wani ɓangare na ƙoƙarin zama cikin shirin ko ta kwana, rahotanni sun bayyana cewa, Babban Sufeton ‘yan sanda Usman Alƙali Baba ya ba da umarnin dukkan kwamishinonin ‘yan sanda da manyan jami’an tsaro na rundunar ‘yan sanda ta ƙasa su ƙara ɗaukar matakan tsaro, domin tabbatar da ganin an hana ɓatagari sakewa da aikata wata ɓarna da za ta iya haifar da barazanar tsaro ga rayuka da dukiyoyin jama’a.

Yayin da haɗin gwiwar sauran rundunonin tsaro ke cikin shiri, da gudanar da bincike da sintiri a wuraren da aka san mavoyar ɓatagari ce da nufin kai musu samame.

A wannan karon dai ya kamata a jinjinawa jami’an tsaro, da shugabanninsu, bisa saurin ɗaukar matakan da aka yi, domin kaucewa zarge-zarge da za su iya fitowa daga baya idan har abin Allah ya kiyaye wani abu ya faru, saboda sakaci da rashin ɗaukar shawara.

Kamar dai abin da ya faru a lokacin mummunan harin da ‘yan ta’adda suka kai gidan gyaran hali na Kuje a Babban Birnin Tarayya Abuja, duk kuwa da rahotannin da aka fitar da kiran da aka yi na ɗaukar mataki.

Abubuwan sakaci da takaici da dama sun faru a ƙasar nan, inda daga bisani ake ɗora alhakin faruwar su kan sakacin jami’an tsaro da rashin ɗaukar matakin da ya dace, na kiyaye afkuwar haka a kan lokaci.

Ana zargin jami’an tsaron ƙasar nan da ‘yan ihu bayan hari, ba sa tashi zuwa wajen da ɓarna ke faruwa sai bayan ta afku, a je ana cike ciken takardu da kafa kwamitocin bincike. Amma ba a tunkarar matsala tun kafin ta auku, da nufin murƙushe ta, ko hana ta faruwa baki ɗaya.

Ko da ya ke tilas wani lokaci mu bai wa jami’an tsaro musamman na ‘yan sanda, waɗanda su ne alhakin kula da harkokin tsaro na cikin gida ke hannun su, uzuri saboda duk da ƙwarewar su da himmar da suke da ita, suna fama da matsalolin rashin kayan aiki masu inganci, rashin wadatar ma’aikata, rashin samun ingantattun rahotannin sirri a kan lokaci. Sannan da uwa uba rashin ƙwarin gwiwa wajen biyan haƙƙoƙin jami’an tsaro yadda ya kamata.

Duk da haka za mu iya cewa, wannan ba hujja ba ce ta rashin mayar da hankali ga haƙƙin da dokar ƙasa ta ɗora musu, na tabbatar da bin doka da oda, da kiyaye rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa da baƙi. Dole ne jami’an tsaro na ‘yan sanda su zama tsayayyu a kan ayyukan su, ba tare da bari son zuciya ko baragurbin ‘yan ƙasa sun ɓata musu suna ba.

Ya zama wajibi gwamnati da jami’an tsaro da ayyukan su ke shafar rayuwar al’umma su hada hannu wajen tabbatar da ganin sun rufe duk wata ƙofa da wasu ɓatagari za su yi amfani da ita su haifar da rashin tsaro da taɓarɓarewar zaman lafiya.

Yana da matuƙar muhimmanci a yi amfani da dabaru na siyasa, diflomasiyya, da shugabanci wajen aiki tare da farar hula,
don sauƙaƙa nauyin da ke kan jami’an ‘yan sanda.

Wasu rahotannin a makon da ya gabata sun rawaito cewa tsohon Ministan Tsaron Nijeriya Manjo Janar Theophilus Danjuma mai ritaya ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su tashi su nemi makamin kare kansu, daga ta’addancin da ke faruwa a ƙasar nan, tun da jami’an tsaro sun kasa ba su kariya da suke buƙata, bayanin da ya ƙara jawo muhawara mai zafi a tsakanin ‘yan Nijeriya, musamman ƙwararru masana harkokin tsaro.

Ko da ya ke ba shi ne mutum na farko da ya fara furta irin haka ba, amma fitowar maganar daga babban mutum masanin tsaro kamar Janar Danjuma, abu ne da dole ya dauki hankalin ‘yan Nijeriya. Sannan zuwan maganar a lokaci na siyasa da zazzafar muhawarar da ake yi game da batun takarar Musulmi da Musulmi, da kuma boren da haɗin gwiwar Kiristan Arewa kan wannan matsaya, dole a ga rashin cancantar wannan magana tasa.

Saboda magana ce mai harshen damo, da ke iya tunzura magoya bayansa da jama’ar da ya ke wakilta.

Za a iya cewa ma ya fara zama gama garin magana a wuraren da ta’addanci da rikice-rikice suka yi tsamari. Na tava wani rubutu a wannan shafin inda na shawarci ‘yan siyasa da masu faɗa a ji su guji amfani da halin taɓarɓarewar tsaro da ƙasar nan ke ciki, suna tayar da fitina da angiza jama’a su ɗauki makamin kare kai, a maimakon ba da gudunmawa ga hanyoyin inganta tsaro da taimakawa hukumomi, bisa irin ƙwarewa da damar da suke da ita.

A yayin da wasu ke ganin tilas ce ke sa wasu yin irin wannan furuci ga raunanan talakawansu waɗanda ba su da ƙarfi da gogewar yin fito na fito da masu riƙe da muggan makamai da ƙeƙasasshiyar zuciya. Wasu na ganin yin waɗannan kalamai a yayin da lamura suka rincaɓe, babbar gazawa ce ga hukumomi, sannan barazana ce mai ƙarfi ga sha’anin tsaron ƙasar nan.

Duk da ya ke muna sane da cewa, jami’an tsaron ƙasar nan suna fuskantar manyan ƙalubale masu yawa da suka haɗa da bazuwar ƙungiyoyin ta’adda da ƙarancin jami’an tsaro.

Ashe ba za mu yi aiki da hankali ba wajen nazarin wasu hanyoyin da za su iya kawo sauƙi wajen magance wannan matsala ba, kamar horar da matasa ‘yansa kai da za su yi aiki ƙarƙashin kulawar jami’an tsaron gwamnati da ba da gudunmawa wajen tunkarar ta’addanci a ƙauyuka da lunguna ba, kamar yadda ya ke faruwa a Jihar Borno game da ayyukan ‘yan ƙato da gora.

Mai ya sa ‘yan siyasar mu da masu irin waɗannan maganganu na nuna gazawar jami’an tsaron mu ba za su yi tunanin illar da kalaman su za su yi wa al’umma ba.

Lallai gwamnati da sauran ‘yan Nijeriya su gane cewa, gargaɗin da Amurka ta yi wa Nijeriya ba wasa ba ne, musamman a wannan lokaci na siyasa, ‘yan ta’addan da muke raina yawan su ko damarsu, za su iya aikata abin da zai girgiza kowa.

Don haka jama’a su tashi tsaye wajen kula da yankunansu, da bayar da rahoton duk wani abu da ba su amince da shi ba, ga jami’an tsaro. Kuma a cire tsoro a shiga aikin sa kai, da banga ƙarƙashin rundunonin tsaro na gwamnati, don kakkaɓe vata garin da suke lalata mana rayuwa suke durƙusar da tattalin arzikinmu.

Amma ba na goyon bayan a je a nemi makamai a saya a tara, kamar yadda ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ke yi, domin kare kai. Wannan shawara mai haɗari ce sosai, kuma ina shawartar jama’a su yi hattara. Amma a haɗa kai, a cire tsoro, a bai wa hukumomi haɗin kai.

Allah ya taimake mu, ya ba mu zaman lafiya da tsaro a Nijeriya baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *