Me ƙasar Sin ta kawo wa duniya a shekarar da ta gabata?

CRI HAUSA

Yau Litinin hukumar ƙididdiga ta ƙasar Sin, ta gabatar da rahoton ƙididdiga kan ci gaban ƙasar Sin a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al’ummar ƙasa a shekarar 2021.

Rahoton ya cewa, duk da ƙalubaloli da dama da ake fuskanta a ciki da wajen ƙasar Sin ta fuskar tattalin arziki, amma ƙasar Sin ta samu karuwar tattalin arziki da kaso 8.1 cikin ɗari, kana yawan ƙaruwar GDP na ko wane mutum ya kai kaso 8 cikin dari. Ci gaban tattalin arzikin ƙasar Sin ya ƙara babban kuzari kan tattalin arzikin duniya, wanda ake ƙoƙarin farfaɗo da shi.

Ban da haka kuma, tattalin arzikin ƙasar Sin yana mara wa tattalin arzikin duniya baya sosai. A shekarar 2021, gudummawar da ƙasar Sin ta bayar ga ci gaban tattalin arzikin duniya ta kai kaso 25 cikin ɗari. Jimilar kuɗaɗen shigi da ficin kayayyaki ta kai kuɗin Sin Yuan triliyan 39.1 a ƙasar Sin, wanda ya ƙaru da kaso 21.4 cikin ɗari bisa makamancin lokaci na shekarar 2020, don haka ƙasar Sin ta shafe shekaru 5 a jere tana zama ta farko a duniya a fannin cinikin kayayyaki. Hakan ya nuna cewa, ƙasashen duniya na buƙatar kayayyaki ƙirar ƙasar Sin. Al’ummar ƙasar Sin na sayen kayayyaki daga sassa daban daban duniya, abin da ke nuna ƙarin buƙatunsu.

Har ila yau, kasuwar ƙasar Sin ta ƙara samar wa kamfanonin ƙasa da ƙasa damar samun ci gaba. A shekarar 2021, yawan sabbin kamfanoni masu jarin waje ya kai dubu 61 a ƙasar Sin, wanda ya ƙaru da kaso 23.3 cikin ɗari bisa makamancin lokaci na shekarar 2020.

Duk da rashin tabbas da ake fuskanta a duniya, tattalin arzikin ƙasar Sin yana ci gaba da ƙara ba da tabbaci kan farfaɗo da tattalin arzikin duniya.

Fassarawa: Tasallah Yuan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *